Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 4:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Allah shi yake yin mayalwacin alheri. Domin haka Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana yi wa masu tawali'u alheri.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Amma yakan ba mu alheri a yalwace. Shi ya sa Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girman kai amma yakan ba da alheri ga masu tawali’u.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 4:6
34 Iomraidhean Croise  

Amma Hezekiya ya ƙasƙantar da kansa saboda girmankan da ya yi, shi da mazaunan Urushalima, saboda haka hasalar Ubangiji ba ta faɗa musu a kwanakin Hezekiya ba.


Amma sa'ad da yake wahala, sai ya roƙi jinƙan Ubangiji Allahnsa, ya ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa.


Addu'arsa, da yadda Allah ya karɓi roƙonsa, da dukan zunubinsa, da rashin amincinsa, da wuraren da ya gina masujadai, ya kafa Ashtarot da siffofi, kafin ya ƙasƙantar da kansa, suna nan a rubuce a littafin Hozai.


Bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji yadda tsohonsa, Manassa, ya yi ba, amma shi Amon ya yi ta yin zunubi a kai a kai.


da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allah, sa'ad da ka ji maganarsa a kan wurin nan da mazaunan wurin, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana, ka yayyage tufafinka ka yi kuka a gabana, ni kuma na ji ka.


Allah yakan ƙasƙantar da mai girmankai, Yakan ceci mai tawali'u.


Ko da yake Ubangiji yana can Sama, Duk da haka yana kulawa da masu kaɗaici. Masu girmankai kuwa ba za su iya ɓoye kansu daga gare shi ba.


Allah yana tunawa da waɗanda suke shan wuya, Ba ya mantawa da kukansu, Yana kuma hukunta waɗanda suke cutarsu.


Yanzu na sani Ubangiji yake gāba da sauran alloli duka, gama ya ceci Isra'ilawa daga tsanantawar da Masarawa suka yi musu.”


Tsoron Ubangiji koyarwa ce domin samun hikima. Sai ka zama mai tawali'u kafin ka sami girmamawa.


Ba wanda za a girmama sai mai tawali'u, mutum mai girmankai kuwa yana kan hanyar hallaka.


Kana da tsoron Ubangiji, ka yi tawali'u, za ka arzuta, ka ɗaukaka, ka sami tsawon rai.


Girmankan mutum zai jawo masa ƙasƙanci, amma za a girmama mai tawali'u.


Ba ruwansa da masu girmankai, amma masu tawali'u sukan sami tagomashi a wurinsa.


Girmankan ɗan adam zai ƙare, za a hallakar da fāriyar ɗan adam, Ubangiji ne kaɗai za a ɗaukaka sa'ad da wannan rana ta yi,


“A ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke, Amma da ƙauna mai zurfi zan sāke karɓarki.


Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.


Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin Samaniya, ina ɗaukaka shi, ina kuma girmama shi saboda dukan ayyukansa daidai ne, al'amuransa kuma gaskiya ne. Yakan ƙasƙantar da masu girmankai.”


Domin mai abu akan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.


Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.


Ya firfitar da sarakuna a sarauta, Ya ɗaukaka ƙasƙantattu.


Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”


Ina dai gaya muku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”


Ku ƙasƙantar da kanku ga Ubangiji, shi kuwa zai ɗaukaka ku.


Haka nan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikkilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali'u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali'u alheri.”


Kada ku ƙara yin magana ta girmankai, Ku daina maganganunku na fariya, Gama Ubangiji Allah shi ne masani, Yana kuma auna dukkan aikin da mutum ya yi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan