Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 4:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce, “Wannan ruhu da Allah ya sa a cikinmu yana tsaronmu ƙwarai”?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce ruhun da ya sa yă zauna a cikinmu yana kishi sosai?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 4:5
24 Iomraidhean Croise  

Da yake ya yi ta arzuta da garken tumaki, da na shanu, da iyali masu yawa, Filistiyawa suka ji ƙyashinsa.


Sa'ad da Rahila ta ga ba ta haihuwa, sai ta ji kishin 'yar'uwarta, ta kuma ce wa Yakubu, “Ka ba ni 'ya'ya, in kuwa ba haka ba, zan mutu!”


'Yan'uwansa suka ji kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe al'amarin cikin zuciyarsa.


Amma Onan ya sani zuriyar ba za ta zama tasa ba, saboda haka duk lokacin da ya shiga wurin matar ɗan'uwansa, sai ya zubar da maniyyi a ƙasa don kada ya ba ɗan'uwansa zuriya.


Ubangiji kuwa ya ga muguntar mutum ta ƙasaita a duniya, dukan zace-zacen tunanin zuciyarsa kuma mugunta ne kullayaumin.


Sa'ad da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce, “Ba zan ƙara la'anta ƙasa sabili da mutum ba, ko da yake zace-zacen zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa. Ba zan kuma ƙara hallaka kowane mai rai ba kamar yadda na yi a dā.


Can cikin hamada suka ji kishin Musa Da Haruna, bayin Ubangiji, tsarkaka,


Kada ka damu saboda mugaye, Kada ka yi ƙyashin masu aikata abin da ba daidai ba.


Mugaye sun zaƙu su aikata mugunta, ba su yi wa kowa jinƙai.


Na gane dalilin da ya sa mutane suke aiki ƙwarai don su ci nasara, so suke su fi kowa samu. Wannan ma aikin banza ne harbin iska kawai.


Masarautar Isra'ila ba za ta ƙara jin kishin Yahuza ba, Yahuza kuma ba za ta zama abokiyar gābar Isra'ila ba.


Amma Musa ya ce masa, “Kishi kake yi domina? Da ma jama'ar Ubangiji duka annabawa ne, har ma ya sa Ruhunsa a cikinsu!”


Allah ba kamar mutum ba ne, da zai yi ƙarya, Ba kuwa ɗan mutum ba ne, da zai tuba. Zai cika dukan abin da ya alkawarta, Ya hurta, ya kuwa cika.


To, in waɗanda Maganar Allah ta zo musu ya ce da su alloli (Nassi kuwa ba ya tashi),


Wani Nassi kuma ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”


Nassi ba cewa ya yi Almasihu zuriyar Dawuda ne ba, daga kuma Baitalami yake, ƙauyen da Dawuda ya zauna?”


“Kakannin nan kuwa, da yake suna kishin Yusufu, suka sayar da shi, aka kai shi Masar. Amma Allah na tare da shi,


Su masu aikata rashin adalci ne ƙwarai, da mugunta, da kwaɗayi, da ƙeta. Masu hassada ne, da kisankai, da jayayya, da ha'inci, da kuma nukura gaya matuƙa. Macizan ƙaiƙayi ne,


Don a Nassi an ce da Fir'auna, “Na girmama ka ne musamman, domin in nuna ikona a kanka, domin kuma a sanar da sunana a duniya duka.”


Ashe, ba ku sani ba, jikinku Haikali ne na Ruhu Mai Tsarki wanda yake a zuciyarku, wanda kuka kuma samu a gun Allah? Ai, ku ba mallakar kanku ba ne.


Wace yarjejeniya ce take a tsakanin Haikalin Allah da gumaka? Domin mu haikali ne na Allah Rayayye. Yadda Allah ya ce, “Zan zauna tare da su, in yi yawo a tsakaninsu, Zan kuma kasance Allahnsu, Su kuma su kasance jama'ata.


A cikin Nassi kuwa an hango, cewa Allah zai kuɓutar da al'ummai ta wurin bangaskiya, wato, dā ma can an yi wa Ibrahim bishara cewa, “Ta wurinka za a yi wa dukkan al'ummai albarka.”


Mu kanmu ma dā can mun yi wauta, mun kangare, an ɓad da mu, mun jarabta da muguwar sha'awa da nishaɗi iri iri, mun yi zaman ƙeta da hassada, mun zama abin ƙi, mu kuma mun ƙi waɗansu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan