Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 4:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Kukan yi addu'a ku rasa, don kun yi ta da mugun nufi ne, don ku ɓatar a kan nishaɗinku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Sa’ad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan sha’awace-sha’awacenku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 4:3
25 Iomraidhean Croise  

Ya kuma ce masa. “Da yake ka roƙi wannan, ba ka roƙar wa kanka yawan kwanaki, ko wadata ba, ko kuma ran maƙiyanka, amma ka roƙa a ba ka hikima yadda za ka mallaki jama'a,


Suka yi kira don taimako, amma Allah bai amsa ba, Saboda suna da girmankan mugaye.


Suna kukan neman taimako, amma ba wanda zai iya cetonsu, Za su yi kira ga Ubangiji, amma ba zai amsa ba.


Sa'an nan za ku kira gare ni, amma ba za ku same ni ba. Za ku neme ni a ko'ina, amma ba za ku same ni ba.


Ubangiji yana murna sa'ad da adalai suke yin addu'a, amma yana ƙin hadayun da mugaye suke miƙa masa.


Idan ka ƙi jin kukan matalauci, naka kukan da kake yi na neman taimako, ba za a ji ba.


Ubangiji yana ƙin hadayar da mugaye suka miƙa masa, tun ba wadda suka miƙa ta da mugun nufi ba.


Saboda haka ni Ubangiji na ce, ‘Ga shi, ina kawo musu masifa wadda ba za su iya tsere mata ba, ko da za su yi kuka gare ni ba zan ji su ba.


Don haka kada ka yi wa waɗannan mutane addu'a. Kada ka yi kuka ko addu'a dominsu, gama ba zan kasa kunne gare su ba, ko da sun yi kirana a lokacin wahalarsu.”


Ko da sun yi azumi, ba zan ji kukansu ba, ko da sun miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta sha, ba zan karɓe su ba. Amma zan hallaka su da takobi, da yunwa, da annoba.”


Sa'an nan za su yi kuka ga Ubangiji, Amma Ubangiji ba zai amsa musu ba. Zai ɓoye musu fuskarsa a wannan lokaci, Saboda mugayen ayyukansu.


Kamar yadda na yi kira suka ƙi ji, haka kuma suka yi kira, ni ma na ƙi ji.


Amma Yesu ya amsa ya ce, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Kwa iya shan ƙoƙon da ni zan sha?” Suka ce masa, “Ma iya.”


Amma Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Kwa iya sha da ƙoƙon da ni zan sha? Ko kwa iya a yi muku baftisma da baftismar da za a yi mini?”


Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.


Bayan 'yan kwanaki kaɗan sai ƙaramin ya tattara duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa ƙasa mai nisa. A can ya fallasar da kayansa a wajen masha'a.


Amma da ɗan nan naka ya zo, wanda ya fallasar da dukiyarka a kan karuwai, ga shi, ka yanka masa kiwataccen ɗan maraƙin nan!’


Me yake haddasa gāba da husuma a tsakaninku? Ashe, ba sha'awace-sha'awacenku ne suke yaƙi da juna a zukatanku ba?


Mukan kuma sami duk abin da muka roƙa a gare shi, domin muna bin umarninsa, muna kuma yin abin da yake so.


Wannan ita ce amincewarmu a gabansa, wato, in mun roƙi kome bisa ga nufinsa, sai ya saurare mu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan