Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 4:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Kukan yi marmarin abu ku rasa, sai ku yi kisankai. Kukan yi kwaɗayi, ku kasa samu, sai ku yi husuma da faɗa. Kukan rasa don ba kwa addu'a ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 4:2
14 Iomraidhean Croise  

Ya ce mata, “Domin na yi magana da Nabot Bayezreyele, na ce ya sayar mini da gonar inabinsa, idan kuma yana so, sai in ba shi wata gonar inabi a maimakon tasa, amma ya ce ba zai ba ni gonar inabin ba.”


Yin fashi yakan zama sanadin mutuwar ɗan fashi a koyaushe. Wannan shi ne abin da yakan sami kowane mutum da ya kama sana'ar sata.


mutumin da ba shi da kowa, ba ɗa, ba ɗan'uwa, duk da haka a kullum yana ta fama da aiki. Bai taɓa ƙoshi da wadatar da yake da ita ba. Saboda me yana ta fama da aiki, ya hana wa kansa jin daɗi? Wannan ma aikin banza ne, zaman baƙin cikin ne.


Ahaz ya amsa, ya ce, “Ba zan nemi wata alama ba. Ba zan jarraba Ubangiji ba.”


“Ruwan inabi kuma yana yaudarar mai fariya, Don haka ba ya zama a gida. Haɗamarsa tana da fāɗi kamar Lahira, Kamar kuma mutuwa yake, ba ya ƙoshi. Ya tattara wa kansa al'ummai duka, Ya kwaso wa kansa mutane duka.”


Har yanzu dai ba ku roƙi kome da sunana ba. Ku roƙa, za ku samu, domin farin cikinku ya zama cikakke.”


Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce miki, ‘Sa mini ruwa in sha,’ ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwan rai.”


In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.


Kun hukunta mai adalci, kun kuma kashe shi, bai kuwa yi muku tsayayya ba.


Kowa da yake ƙin dan'uwansa, mai kisankai ne. Ƙun kuwa sani ba mai kisankan da yake da rai madawwami a zauna tare da shi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan