Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 4:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Amma ga shi, kuna fariya ta alfarmar banza da kuke yi. Duk irin wannan fariya kuwa muguwar aba ce.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Ga shi, kuna fariya da taƙama. Duk irin wannan taƙama mugun abu ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 4:16
11 Iomraidhean Croise  

Me ya sa kake fariya da muguntarka, Ya kai, babban mutum? Ƙaunar Allah tana nan a koyaushe.


“Duba, ga mutumin da bai dogara ga Allah Don ya sami zaman lafiyarsa ba. A maimakon haka, sai ya dogara ga wadatarsa. Yana neman zaman lafiyarsa ta wurin muguntarsa.”


Mutanen da suke yin alkawari, ba su cikawa, kamar holoƙo suke, hadirin kaka.


Kada ka yi fāriya a kan abin da za ka yi gobe domin ba ka san abin da zai faru daga yanzu zuwa gobe ba.


“Kin amince da kanki cikin muguntarki, Kina tsammani ba wanda yake ganinki. Hikimarki da saninki suka sa kika ɓata, Kika kuwa ce da kanki, ‘Ni ce Allah, Ba mai kama da ni!’


Fāriyarku ba shi da kyau. Ashe, ba ku sani ba, ɗan yisti kaɗan yake game dukkan curin gurasa?


Amma in kuna da matsanancin kishi da sonkai a zuciyarku, kada ku yi alwashi da haka, kuna saɓa wa gaskiya.


Don kuwa duk abin da yake duniya, kamar su sha'awa irin ta halin mutuntaka, da sha'awar ido, da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ne.


Yadda ta ɗaukaka kanta, ta yi almubazzaranci, Haka ku ma ku saka mata da azaba, da baƙin ciki gwargwadon haka. Tun da yake a birnin zuciyarta ta ce, ‘Ni sarauniya ce, a zaune nake, Ni ba gwauruwa ba ce, Ba ni da baƙin ciki kuma har abada!’


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan