Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 4:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ya ku 'yan'uwana, kada ku kushe wa juna. Kowa ya kushe wa ɗan'uwansa, ko ya ɗora masa laifi, ya kushe wa shari'a ke nan, ya kuma ɗora mata laifi. In kuwa ka ɗora wa shari'a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 ’Yan’uwa, kada ku ɓata wa juna suna. Duk wanda ya zargi ɗan’uwansa ko ya ɗora masa laifi, yana gāba da doka ne yana kuma yin mata shari’a ke nan. In kuwa ka ɗora wa shari’a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 4:11
24 Iomraidhean Croise  

Ka sa waɗanda suke saran waɗansu a ƙaryace, Kada su yi nasara. Ka sa mugunta ta hallaka mutumin da yake ta da zaune tsaye.”


“Kada ku ɗora wa kowa laifi, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yi wa kowa mugun zato, ku ma ba za a yi muku ba. Ku yafe, ku ma sai a yafe muku.


Saboda haka ba ka da wata hujja, kai mutum, ko kai wane ne da kake ganin laifin wani. A yayin da kake ganin laifin wani, ai, kanka kake hukunta wa, don ga shi, kai mai ganin laifin wani, kai ma haka kake yi.


Don ba ta jin shari'ar kawai mutum yake samun kuɓuta ga Allah ba, sai dai masu aikata ta, su ne za su kuɓuta.


To, me kuma za mu ce? Shari'a zunubi ce? A'a, ko kusa! Amma kuwa duk da haka, da ba domin Shari'a ba, da ban san zunubi ba. Da ba domin Shari'a ta ce, “Kada ka yi ƙyashi” ba, da ban san ƙyashi ba.


Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.


Ina tsoro kada watakila in na zo in same ku ba a yadda nake so ba, ku kuma ku gan ni ba a yadda kuke so ba, ko ma a tarar da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da yanke, da tsegunguma, da girmankai, da tashin hankali.


Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da yanke, da kowace irin ƙeta.


Haka kuma matan, lalle su zama natsattsu, ba masu yanke ba, amma masu kamunkai, masu aminci ta kowace hanya.


da marasa ƙauna, da masu riƙo a zuci, da masu yanke, da fajirai, da maƙetata, da maƙiyan nagarta,


Haka kuma, manyan mata su kasance masu keɓaɓɓen hali, ba masu yanke, ko masu jarabar giya ba, su zamana masu koyar da kyakkyawan abu,


Kada fa a yaudare ku, ya 'yan'uwana ƙaunatattu.


Ya 'yan'uwana ƙaunatattu, ku san wannan, wato, kowa yă yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi,


Amma duk mai duba cikakkiyar ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake aikatawa.


Idan lalle kun cika muhimmin umarni yadda Nassi ya ce, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” to, madalla.


A kan misalin shan wuya da haƙuri kuma, 'yan'uwa, ku dubi annabawa ma da suka yi magana da sunan Ubangiji.


Domin haka, sai ku yi haƙuri, 'yan'uwana, har ya zuwa ranar komowar Ubangiji. Ga shi, manomi yana sa rai ga samun amfanin gona mai albarka, yana kuwa haƙuri da samunsa, har a yi ruwan shuka da na kaka.


'Yan'uwa, kada ku yi wa juna gunaguni, don kada a hukunta ku. Ga mai shari'a a bakin ƙofa!


Saboda haka, sai ku yar da kowace irin ƙeta, da ha'inci, da munafunci, da hassada, da kuma kowane irin kushe.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan