Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 3:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Da shi muke yabon Ubangiji Uba, da shi kuma muke zagin mutane waɗanda aka halitta da kamannin Allah.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Da harshe mukan yabi Ubangijinmu da kuma Ubanmu, da shi kuma muke la’antar mutane, waɗanda aka halitta a kamannin Allah.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 3:9
34 Iomraidhean Croise  

Wannan shi ne littafin asalin Adamu. A sa'ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin siffar Allah.


“Duk wanda ya kashe mutum, ta hannun mutum za a kashe shi, gama Allah ya yi mutum cikin siffarsa.


Sa'ad da Dawuda ya kai Bahurim, sai ga wani mutum sunansa Shimai, ɗan Gera, daga iyalin gidan Saul, ya fito yana ta zagi.


Abishai ɗan Zeruya kuwa ya ce, “Ya kamata a kashe Shimai gama ya zagi wanda Ubangiji ya zaɓa ya zama sarki.”


Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, ya ce, “Ya Ubangiji Allah na kakanmu Yakubu, yabo ya tabbata gare ka har abada abadin!


Sa'an nan Dawuda ya ce wa taro duka, “Sai ku yabi Ubangiji Allahnku yanzu.” Taron jama'a kuwa suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu, suka rusuna har ƙasa, suka yi wa Ubangiji sujada, suka kuma girmama sarki.


Maganganunsa suna cike da zage-zage, da ƙarairayi, da barazana, Yana da saurin faɗar maganganun ƙiyayya da na mugunta.


A shirye nake, ya Allah, Na shirya sosai! Zan raira waƙa in yabe ka! Ka farka, ya raina!


Zan yi shelar girmanka, ya Allahna, Sarkina, Zan yi maka godiya har abada abadin.


A kullum zan yabi Ubangiji, Bari talikai duka su yabi sunansa mai tsarki har abada!


Don haka cike nake da murna da farin ciki, Kullum kuwa ina jin kome lafiya yake,


Don haka ba zan yi shiru ba, Zan raira maka yabo, Ya Ubangiji, kai ne Allahna, Zan gode maka har abada.


Zan yi godiya ga Ubangiji kullayaumin, Faufau ba zan taɓa fasa yabonsa ba.


Sa'an nan zan yi shelar adalcinka, Dukan yini kuwa zan yi ta yabonka.


Ka rayar da raina, ya Allah Mai Cetona, Zan kuwa yi shelar adalcinka da farin ciki.


Ka farka, ya raina! Ku farka, molona da garayata! Zan sa rana ta farka!


Zunubi na cikin leɓunansu, maganganunsu na zunubi ne, Da ma a kama su saboda girmankansu, Domin suna la'antarwa, suna ƙarya!


Ba abin da kuke so, sai ku ƙasƙantar da shi daga maƙaminsa na daraja, Kuna jin daɗin yin ƙarairayi. Kuna sa masa albarka, Amma a zuciyarku la'antarwa kuke yi.


Muddin raina, zan yi maka godiya, Zan ta da hannuwana sama, in yi addu'a gare ka.


Zan yi magana a kan adalcinka dukan yini, Saboda an yi nasara da waɗanda suke ƙoƙari su cuce ni, sun ruɗe.


Kai kanka ka sani sau da yawa kakan zagi waɗansu mutane.


Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane sun ce suna mini sujada, amma kalmominsu ba su da ma'ana, zukatansu kuma suna wani wuri dabam. Addininsu ba wani abu ba ne, sai dai dokoki ne da ka'idodin mutane da suka haddace.


Sai ya fara la'anar kansa, yana ta rantse-rantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba.” Nan da nan sai zakara ya yi cara.


Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu'a,


Saboda haka, zuciyata ta yi fari, ina farin ciki matuƙa. Ko da yake kuma ni jiki ne, zan zauna ina sa zuciya,


“Yawan zage-zage da ɗacin baki gare su.”


Namiji kam, bai kamata yă rufe kansa ba, tun da yake shi kamannin Allah ne, abin alfahari ga Allah kuma. Amma mace abar taƙamar namiji ce.


Yabo yā tabbata ga Allahn Ubangijinmu Yesu Almasihu, da Ubansa kuma, wanda ya yi mana albarka da kowace albarka ta Ruhu, basamaniya, a cikin Almasihu,


Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Allah Ubanmu, shi ne a kula da gwauraye mata, da marayu a cikin ƙuntatarsu, a kuma a keɓe kai marar aibi daga duniya.


Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba!


Godiya ta tabbata a gare shi, shi wanda yake Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurin tsananin jinƙansa ya sāke haifuwarmu, domin mu yi rayayyen bege, ta wurin albarkacin tashin Yesu Almasihu daga matattu,


Suka tafi gona, suka ɗebo inabi, suka matse, suka yi biki a gidan gunkinsu. Suka ci, suka sha, suka zazzagi Abimelek.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan