Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 3:8 - Littafi Mai Tsarki

8 amma ba ɗan adam ɗin da zai iya sarrafa harshe, ai, mugunta ne da ba ta hanuwa, a cike yake da dafi mai kashewa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 amma ba mutumin da zai iya ya sarrafa harshe. Mugu ne marar hutu, cike da dafi mai kisa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 3:8
13 Iomraidhean Croise  

Harsunansu kamar macizai masu zafin dafi, Kalmominsu kuwa kamar dafin gamsheƙa ne.


Kalmominsa sun fi mai taushi, Amma ƙiyayya tana a zuciyarsa, Kalmominsa sun fi mai sulɓi, Amma suna yanka kamar kakkaifan takobi.


Raina yana tsakiyar zakoki, Na kwanta a tsakiyar waɗanda suka yi niyyar cinye mutane. Haƙoransu kamar māsu da kibau suke, Harsunansu masu kaifi ne kamar takobi.


Cike suke da dafi kamar macizai, Sukan toshe kunnuwansu kamar kuraman gamsheƙa,


Ji abin da suke fada! Harsunansu suna kama da takuba a bakinsu, Duk da haka suna ta tambaya, suna cewa, “Wa zai ji mu?”


Mutumin da yakan yi tunanin mugunta, ya kuma hurta ta, kada ya sa zuciya ga samun abin kirki, sai dai bala'i kaɗai.


Idan maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi kuma, ba shi da wani amfani.


“Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗen kabari ne, Maganarsu ta yaudara ce.” “Masu ciwon baki ne.”


Ruwan inabinsu dafin macizai ne. Da mugun dafin kumurci.


Harshe ma wuta ne fa! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata dukan jiki, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa Gidan Wuta ne yake zuga shi.


Don kuwa ana iya sarrafa kowace irin dabba, da tsuntsu, da masu jan ciki, da halittar ruwa, ɗan adam har yā sarrafa su ma,


Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala'ikunsa ma aka jefa su tare da shi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan