Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 3:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Harshe ma wuta ne fa! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata dukan jiki, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa Gidan Wuta ne yake zuga shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Harshe ma wuta ne! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata mutum gaba ɗaya, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa jahannama ce take zuga shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 3:6
62 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan Absalom ya juya wajen Ahitofel, ya ce, “To, ka kawo shawararka a kan abin da ya kamata mu yi?”


Isra'ilawa kuma suka amsa wa mutanen Yahuza, suka ce, “Muna da rabo goma a wurin sarki Dawuda fiye da ku, don me kuka raina mu? Ba mu ne muka fara maganar komowar sarki ba?” Amma maganar mutanen Yahuza ta fi ta mutanen Isra'ila zafi.


Abaija fa, da jama'arsa suka karkashe su, mugun kisa. Mutum dubu ɗari biyar (500,000) zaɓaɓɓu na Isra'ila, aka karkashe.


Harsunansu kamar macizai masu zafin dafi, Kalmominsu kuwa kamar dafin gamsheƙa ne.


Sukan wasa harsunansu kamar takuba, Sukan kai bāra da mugayen maganganu kamar kibau.


Amsa magana da tattausan harshe takan kwantar da hasala, amma magana da kakkausan harshe takan kuta fushi.


Mutumin da yake jin daɗin yin mugunta yakan tafi yawon nemanta, mugayen maganganunsa ƙuna suke kamar wuta.


Za su nisanta ka da matan mutane, daga kuma mata masu maganganun alfasha.


Ana iya ganin ikon Allah da ɗaukakarsa daga nesa! Wuta da hayaƙi suna nuna fushinsa. Ya yi magana, maganarsa tana ƙuna kamar wuta.


Dukanku da kuke ƙulle-ƙullen hallaka juna Ƙulle-ƙullenku za su hallaka ku! Ubangiji kansa zai sa wannan ya faru, Za ku gamu da mummunar ƙaddara.


Na ji mutane da yawa suna sa mini laƙabi cewa, ‘Razana ta kowace fuska,’ Suna cewa, ‘Mu la'anta shi! Mu la'anta shi!’ Har ma da abokaina shaƙiƙai Suna jira su ga fāɗuwata. Suka ce, ‘Watakila a ruɗe shi, Sa'an nan ma iya rinjayarsa Mu ɗauki fansa a kansa.’


Saboda haka, in ji Ubangiji, ‘Zan kawar da kai daga duniya. Za ka mutu a wannan shekara domin ka kuta tayarwa ga Ubangiji.’ ”


Sai ɗan Ba'isra'iliyar ya saɓi sunan Allah. Aka kai shi wurin Musa. Sunan mahaifiyar kuwa Shelomit 'yar Dibri na kabilar Dan.


Waɗannan mata sukan gayyaci mutanen zuwa wajen shagalin tsafinsu. Isra'ilawa kuwa sukan ci abinci, su kuma yi sujada ga gumaka.


Ku tuna fa, su ne, ta wurin shawarar Bal'amu, suka yaudari Isra'ilawa, suka saɓi Ubangiji cikin maƙidar Feyor, har annoba ta fasu a jama'ar Ubangiji.


Amma da Farisiyawa suka ji haka sai suka ce, “Ai, da ikon Ba'alzabul sarkin aljannu kawai, wannan yake fitar da aljannu.”


Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.


Ba abin da yake shiga mutum daga waje yă ƙazanta shi, sai abin da yake fita, yake ƙazanta shi.


Sai ya yi kira ya ce, ‘Baba Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiko Li'azaru ya tsoma kan yatsarsa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba nake sha a cikin wannan wuta.’


Har ma a cikinku waɗansu mutane za su taso, suna maganganun da ba sa kan hanya, don su jawo masu bi gare su.


Sai Bitrus ya ce, “Kai, Hananiya, ta ƙaƙa Shaiɗan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya, ka kuma ɓoye wani abu daga kuɗin gonar?


Sai suka gabatar da masu shaidar zur, suka ce, “Mutumin nan ba ya rabuwa da kushe tsattsarkan wurin nan, da kuma Attaura,


“Idan ɗan'uwanka, wato ɗan mahaifiyarka, ko ɗanka, ko 'yarka, ko ƙaunatacciyar matarka, ko amininka ya rarrashe ka a asirce, yana cewa, ‘Bari mu tafi mu bauta wa gumaka waɗanda ku da ubanninku ba ku san su ba,’


Lalle ne a kwaɓe su, tun da yake suna jirkitar da jama'a gida gida, ta wurin koyar da abin da bai kamata ba, don neman ƙazamar riɓa.


Ba kuma su ne kuke saɓon sunan nan mai girma da ake kiranku da shi ba?


Don kuwa ana iya sarrafa kowace irin dabba, da tsuntsu, da masu jan ciki, da halittar ruwa, ɗan adam har yā sarrafa su ma,


Da farko dai lalle ne ku fahimci wannan, cewa a can zamanin ƙarshe masu ba'a za su zo suna ba'a, suna biye wa muguwar sha'awarsu,


Saboda haka, in na zo zan tabbatar masa da abin da yake yi, yana surutu game da mu, yana ɓaɓɓata mu. Wannan ma bai ishe shi ba, har ya ƙi yi wa 'yan'uwa maraba, yana kuma hana masu so su marabce su, yana fitar da su daga ikkilisiya.


Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala'ikunsa ma aka jefa su tare da shi.


Tana kuma yaudarar mazaunan duniya, da abubuwan al'ajabin nan da aka yardar mata ta yi a gaban dabbar nan, tana umartarsu, su yi wata siffa saboda dabbar nan wadda aka yi wa rauni da takobi, ta kuwa rayu.


Fitila ba za ta ƙara haskakawa a cikinki ba, Ba kuma za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba, Don attajiranki, dā su ne ƙusoshin duniya, An kuma yaudari dukkan al'ummai da sihirinki.


Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan