Yaƙub 3:5 - Littafi Mai Tsarki5 Haka ma harshe yake, ga shi, ɗan ƙaramin abu ne, sai manyan fariya! Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake kunna wa babban jeji wuta! Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20205 Haka ma harshe yake, ga shi ɗan ƙanƙanin gaɓar jiki ne, amma sai manyan fariya. Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake ƙuna wa babban jeji wuta mana. Faic an caibideil |
Yanzu, idan kuna so, sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi ƙasa, ku yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa. Idan kun yi haka, da kyau. Amma idan ba ku yi sujadar ba, nan take za a jefa ku a tanderun gagarumar wuta, in ga ko wane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”