Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 3:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Ku dubi jiragen ruwa kuma, ko da yake suna da girma haka ƙaƙƙarfar iska kuma tana kora su, duk da haka, da ɗan ƙaramin ƙarfe ne matuƙi yake juya su duk inda ya nufa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Ko kuwa misali, mu dubi jiragen ruwa, mana. Ko da yake suna da girma ƙwarai kuma iska mai ƙarfi ce take tura su, ana tuƙa su da ɗan ƙaramin sandan ƙarfe ne zuwa duk inda mai tuƙin jirgin yake so.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 3:4
8 Iomraidhean Croise  

Amma Ubangiji ya aika da iska mai ƙarfi a tekun, hadirin ya tsananta ƙwarai har jirgin yana bakin farfashewa.


Kowane abu Ubana ne ya mallakar mini. Ba kuwa wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban sai Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so ya bayyana wa.


Sai ga wani babban hadiri ya taso a teku, har raƙuman ruwa suka fara shan kan jirgin, amma yana barci.


Amma jarumin soja, ya fi mai da hankali ga maganar mai tuƙin jirgin da kuma ta mai jirgin, a kan abin da Bulus ya faɗa.


Ga misali, idan mun sa linzami a bakin doki, don mu bi da shi, mukan sarrafa dukan jikinsa ma.


Haka ma harshe yake, ga shi, ɗan ƙaramin abu ne, sai manyan fariya! Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake kunna wa babban jeji wuta!


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan