Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 3:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Domin dukanmu muna yin kuskure da yawa. In kuwa mutum ba ya shirme a maganarsa, to, shi cikakken mutum ne, yana kuwa iya kame duk sauran gaɓoɓinsa ma.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Dukanmu mukan yi tuntuɓe a hanyoyi dabam-dabam. In wani bai taɓa yin kuskure a cikin maganarsa ba, shi cikakke ne, yana kuma iya ƙame dukan jikinsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 3:2
29 Iomraidhean Croise  

“Idan jama'arka sun yi maka zunubi, gama ba mutumin da ba ya yin zunubi, har ka yi fushi da su, ka kuwa bashe su a hannun abokan gāba, har suka kwashe su zuwa bauta a wata ƙasa mai nisa,


“Sa'ad da suka yi maka zunubi (gama ba wani ɗan adam da ba ya yin zunubi), ka kuwa yi fushi da su, har ka bashe su a hannun magabtansu, magabtansu suka kakkama su suka kai wata ƙasa ta nesa ko ta kusa,


Fushi kake yi da Allah, kana ƙinsa.


To, ku yi nisa da mugun baki, Da faɗar ƙarairayi.


Na ce, “Zan yi hankali da abin da nake yi, Don kada harshena yă sa ni zunubi, Ba zan ce kome ba sa'ad da mugaye suke kusa.”


Bisa ga yawan surutunka, mai yiwuwa ne ƙwarai ka yi zunubi, amma idan kai mai la'akari ne, sai ka yi shiru.


Ka lura da irin abin da kake faɗa don ka kiyaye ranka. Mutumin da bai kula da maganarsa ba, yakan hallakar da kansa.


Wane ne zai iya cewa lamirinsa garau yake, har da zai ce ya rabu da zunubinsa?


Idan ba ka so ka shiga wahala, ka lura da abin da kake faɗa.


Ba wani mutum a duniyan nan wanda yake aikata abin da yake daidai dukan lokaci, ba tare da yin kuskure ba.


Dukanmu muka cika da zunubi har ayyukanmu mafi kyau ƙazamai ne duka. Saboda zunubanmu, muka zama kamar busassun ganyaye waɗanda iska take faucewa ta tafi da su.


sai firist ya dudduba, idan tabban toka-toka ne, mawanki ne ya faso a fatar, shi tsarkakakke ne.


Ku macizai! Yaya za ku iya yin maganar kirki, alhali kuwa ku mugaye ne? Don abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.


Maganarka ce za ta kuɓutar da kai, ko kuma ta hukunta ka.”


Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Babu wani mai adalci, babu, ko ɗaya,


Sai na ga, ashe, ya zama mini ka'ida, in na so yin abin da yake daidai, sai in ga mugunta tare da ni.


Amma ina azabta jikina ne, don in bautar da shi, kada bayan da na yi wa waɗansu wa'azi, ni da kaina a yar da ni.


Amma Nassi ya kulle kowa a cikin zunubi, don albarkar da aka yi alkawari saboda gaskatawa da Yesu Almasihu, a ba da ita ga masu ba da gaskiya.


Don halin mutuntaka gāba yake yi da Ruhu, Ruhu kuma yana gāba da halin mutuntaka. Waɗannan biyu gāba suke yi da juna, har ba kwa iya yin abin da kuke so.


Shi ne kuwa muke sanarwa, muna yi wa kowane mutum gargaɗi, muna kuma koya wa kowane mutum da matuƙar hikima, da nufin mu miƙa kowane mutum cikakke a cikin Almasihu.


Abafaras wanda yake ɗaya daga cikinku, bawan Almasihu Yesu, yana gaishe ku, a kullum yana yi muku addu'a da himma, ku dage, kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.


yă kamala ku da kowane irin kyakkyawan abu, domin ku aikata nufinsa, yă kuma aikata a cikinmu abin da yake faranta masa rai ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka tā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin, Amin.


In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne.


Sai kuma jimiri ya yi cikakken aikinsa, domin ku zama kamilai cikakku kuma, ba ku gaza da kome ba.


Duk wanda yake kiyaye dukkan Shari'a, amma ya saɓa a kan abu guda, ya saɓi Shari'a gaba ɗaya ke nan.


Domin, “Duk mai so ya more wa zamansa na duniya da alheri, Sai ya kame bakinsa daga ɓarna, Ya kuma hana shi maganar yaudara.


Bayan kun sha wuya kuma ta ɗan lokaci kaɗan, Allah mai alheri duka, wanda ya kira ku ga samun madawwamiyar ɗaukakarsa a cikin Almasihu, shi kansa zai kammala ku, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan