18 Daga irin salama wanda masu sulhuntawa suke shukawa akan girbe adalci.
18 Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.
Waɗanda suke yin 'ya'ya da tsufansu, A kullum kuwa kore shar suke, Suna da ƙarfinsu kuma.
A ainihi mugaye ba su cin ribar kome, amma idan ka yi abin da yake daidai, ka tabbata za a sāka maka da alheri.
Adalai za su arzuta, kamar ganyaye da bazara, amma waɗanda suke dogara ga dukiyarsu za su karkaɗe kamar ganyaye da kaka.
Adalci yana rayar da mutum, wanda yake da hikima kuma yakan ceci rayuka.
Ku shuka wa kanku adalci, Ku girbe albarkun ƙauna, Ku yi kautun saurukanku, Gama lokacin neman Ubangiji ya yi, Domin ya zo, ya koya muku adalci.
Dawakai sukan yi sukuwa a duwatsu? Ana huɗan teku da garmar shanu? Duk da haka kuka mai da adalci dafi, Kuka mai da nagarta, mugunta.
“Albarka tā tabbata ga masu ƙulla zumunci, domin za a ce da su 'ya'yan Allah.
Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare.
Wanda ya yi shuka a kwaɗayin son zuciyarsa, ta wurin son zuciya zai girbi ruɓa. Wanda ya yi shuka a Ruhu, ta wurin Ruhu zai girbi rai madawwami.
kuna da cikakken sakamakon aikin adalci da yake samuwa ta wurin Yesu Almasihu, wannan kuwa duk domin ɗaukakar Allah ne, da yabonsa.
Ai, kowane irin horo, a lokacin shansa, abu ne mai baƙin ciki, ba na farin ciki ba. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.
don fushin mutum ba ya aikata adalci.