11 Ashe, marmaro ɗaya ya iya ɓuɓɓugowa da ruwan daɗi da na zartsi ta ido guda?
11 Ruwa mai kyau da kuma ruwan gishiri zai iya fito daga maɓulɓula ɗaya?
Kamar yadda rijiya take da ruwa garau, Haka Urushalima take da muguntarta, Ana jin labarin kama-karya da na hallakarwa a cikinta, Kullum akwai cuce-cuce, da raunuka a gabana,
Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba!
Ya 'yan'uwana, ashe, ɓaure yana iya haifar zaitun? Ko kuwa inabi ya haifi ɓaure? Haka kuma, ba dama a sami ruwan daɗi a idon ruwan zartsi.