Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 3:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Daga wannan baki guda yabo da la’ana suke fitowa. ’Yan’uwana, wannan bai kamata yă zama haka ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 3:10
14 Iomraidhean Croise  

Abimelek kuwa ya kira Ibrahim, ya ce masa, “Me ke nan ka yi mana? Wane laifi na yi maka, da za ka jawo bala'i mai girma haka a kaina da mulkina? Ka yi mini abin da bai kamata a yi ba.”


Ta ce masa, “Haba, wana, kada ka ƙasƙantar da ni, gama ba a yin haka a cikin Isra'ila, kada ka yi halin dabba.


Shari'ar shugabannin ƙasar ta cin hanci ce. Firistocinta suna koyarwa don neman riba, Haka kuma annabawa suna annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna dogara ga Ubangiji, suna cewa, “Ai, Ubangiji yana tsakiyarmu, Ba masifar da za ta same mu.”


Ku sa wa masu tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, kada ku la'ance su.


don har a yanzu ku masu halin mutuntaka ne. Muddin akwai kishi da jayayya a tsakaninku, ashe, ku ba masu halin mutuntaka ba ne, kuna kuma aikata halin mutuntaka?


Banda haka kuma sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida gida. Ba ma kawai masu zaman banza za su zama ba, har ma sai su zama matsegunta, masu shishigi, suna faɗar abin da bai kamata ba.


Kada fa a yaudare ku, ya 'yan'uwana ƙaunatattu.


Ya 'yan'uwana ƙaunatattu, ku san wannan, wato, kowa yă yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi,


Ya ku 'yan'uwana, kada yawancinku su zama masu koyarwa, domin kun sani, mu da muke koyarwa za a yi mana shari'a da ƙididdiga mafi tsanani.


Ashe, marmaro ɗaya ya iya ɓuɓɓugowa da ruwan daɗi da na zartsi ta ido guda?


Da shi muke yabon Ubangiji Uba, da shi kuma muke zagin mutane waɗanda aka halitta da kamannin Allah.


Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka, sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan