Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 2:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan, Shari'a kuma ta same ku da laifin keta umarni.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Amma in kuka nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan shari’a kuma ta same ku da laifi a matsayin masu karya doka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 2:9
13 Iomraidhean Croise  

“Ku yi gaskiya da adalci cikin shari'a, kada ku ma ku yi wa matalauci son zuciya, ko ku goyi bayan mawadaci.


Sa'ad da kuwa ya zo zai faɗakar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci.


A cikinku wa zai iya haƙƙaƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya nake faɗa, to, don me ba kwa gaskata ni?


Su kuwa da suka ji haka suka fita da ɗaya ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, aka bar Yesu shi kaɗai, da matar tsaye a tsakiya.


Sai Bitrus ya kāda baki ya ce, “Hakika na gane lalle Allah ba ya tara,


Ai, ba wani ɗan adam da zai sami kuɓuta ga Allah ta kiyaye ayyukan Shari'a, tun da yake ta Shari'a ne mutum yake ganin laifinsa.


In kuwa kowa yana yin annabci, wani kuma marar ba da gaskiya ko jahili ya shigo, sai maganar kowa ta ratsa shi, ya kamu a ransa ta maganar kowa,


Gama ni ta wurin Shari'a matacce ne ga Shari'a domin in rayu ga Allah.


Kada ku nuna bambanci cikin shari'a, ko babban mutum ne ko talaka, duka biyu za ku ji su. Kada ku ji tsoron fuskar mutum, gama shari'a ta Allah ce. In kuwa shari'a ta fi ƙarfinku, sai ku kawo ta wurina, ni kuwa zan yanke ta.’


Duk mai aikata zunubi ya yi tawaye ke nan. Zunubi tawaye ne.


don ya zartar da hukunci kan kowa, yă kuma tabbatar wa marasa bin Allah dukan aikinsu na rashin bin Allah, da suka aikata ta hanyar rashin bin Allah, da kuma baƙaƙen maganganu da masu zunubi marasa bin Allah suka yi game da shi.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan