Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 2:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Idan lalle kun cika muhimmin umarni yadda Nassi ya ce, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” to, madalla.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 2:8
23 Iomraidhean Croise  

amma Ubangiji ya ce wa tsohona, Dawuda, ya ji daɗin niyyar da ya yi ta gina Haikali,


Sa'an nan suka ce wa junansu, “Ba mu kyauta ba. Yau ranar albishir ce, idan mun yi shiru, mun jira har safe, wani mugun abu zai same mu. Domin haka bari mu tafi mu faɗa a gidan sarki.”


Kada ya ɗaukar wa kansa fansa a kan wani ko ya yi ta ƙinsa, amma ya ƙaunaci sauran mutane kamar yadda yake ƙaunar kansa. Ni ne Ubangiji.


Amma ku ɗauke shi tankar ɗan ƙasa, ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.


Ubangiji kuwa ya amsa ya ce, “Daidai ne ka yi fushi?”


Amma Allah ya ce masa, “Daidai ne ka yi fushi saboda 'yar kurangar?” Yunusa ya amsa, “Hakika, daidai ne a gare ni in yi fushi, har ma in yi fushin da ya isa in mutu!”


Na biyu kuma kamarsa yake, ‘Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.’


Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangidanka.’


Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangijinka.’


Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.”


Ƙauna ba ta cutar maƙwabci saboda haka ƙauna cika Shari'a ce.


Don duk Shari'a an ƙunshe ta ne a kalma guda, wato, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”


Ku ɗauki wahalar juna, ta haka za ku cika shari'ar Almasihu.


Amma kuwa kun kyauta da kuka taya ni cikin ƙuntatata.


A game da ƙaunar 'yan'uwa kuma, ba lalle sai wani ya rubuto muku ba. Ai, ku kanku ma, Allah ya koya muku ku ƙaunaci juna.


Amma duk mai duba cikakkiyar ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake aikatawa.


Saboda haka, maganarku da aikinku su kasance irin na mutanen da za a yi wa shari'a bisa ga ka'idar 'yanci.


Ka gaskata Allah ɗaya ne? To, madalla. Ai, ko aljannu ma sun gaskata, amma suna rawar jiki don tsoro.


Ya ku 'yan'uwana, kada ku kushe wa juna. Kowa ya kushe wa ɗan'uwansa, ko ya ɗora masa laifi, ya kushe wa shari'a ke nan, ya kuma ɗora mata laifi. In kuwa ka ɗora wa shari'a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne.


Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan