bayan ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antakiya. Shekara sur suna taruwa da Ikkilisiya, suna koya wa mutane masu yawan gaske. A Antakiya ne aka fara kiran masu bi da suna Kirista.
Na kuma sha gwada musu azaba a dukan majami'u, ina ƙoƙarin sa su yin saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.”
ko da yake dā can sāɓo nake yi, ina tsanantarwa, ina wulakantarwa, duk da haka, sai dai aka yi mini jinƙai, domin na yi haka ne da jahilci saboda rashin bangaskiya.