Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 2:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa muku ba? Ba su ne kuwa suke janku zuwa gaban shari'a ba?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 2:6
38 Iomraidhean Croise  

Saboda zalunci da rashin kula da matalauta, Da ƙwace gidajen da waɗansu suka gina.


Yakan ragargaza kāsasshe, Yă gwada masa ƙarfi, yă ci nasara a kansa.


Amma kana gani, kana kuma lura da masu shan wuya, da masu ɓacin rai, Koyaushe kuma a shirye kake ka yi taimako. Mutum wanda ba shi da mai taimako yakan danka kansa gare ka, Gama kullum kakan taimaki masu bukata.


Mugaye suna fāriya, suna kuma tsananta wa matalauta, Ɗana tarkon da suka yi yă kama su.


Yakan ɓuya cikin ƙauyuka, Yă jira a can har yă kashe marasa laifi. Yakan yi sanɗa, ya kama kāsassu,


Ubangiji ya ce, “Amma zan zo yanzu, Domin ana zaluntar masu bukata, Waɗanda aka tsananta musu kuma, suna nishi don zafi. Zan ba su zaman lafiya da suke nema!”


Suna yi wa shirye-shiryen kāsasshe dariya, Saboda yana dogara ga Ubangiji.


Wanda ya zalunci matalauci ya zargi Mahaliccinsa ke nan, amma nuna alheri ga matalauci yin sujada ne.


Wanda ya yi wa matalauci ba'a, Mahaliccinsa yake yi wa zargi. Idan kana murna da hasarar wani, za a hukunta ka.


Matalauci yakan yi roƙo da taushi, maganar matalauci rarrashi ne, amma attajiri yakan yi magana garas.


Idan attajirai kake yi wa kyauta, kana kuma zaluntar matalauta don ka arzuta, kai kanka za ka talauce.


Matalauta su ne bayin attajirai, bawa ne kai ga wanda ka ci bashi a gare shi.


Idan ka ga hukuma na zaluntar talakawa, ba ta yi musu adalci, ba ta kiyaye hakkinsu, kada ka yi mamaki. Kowane shugaba yana da shugaban da yake goyon bayansa. Dukansu biyu suna da goyon bayan manyan shugabanni.


Muka raina shi, muka ƙi shi, Ya daure da wahala da raɗaɗi. Ba wanda ya ko dube shi. Muka yi banza da shi kamar shi ba kome ba ne.


Ku kasa kunne ga wannan, ya ku matan Samariya, Ku da kuka yi ƙiba kamar turkakkun shanu, Ku da kuke wulakanta kasassu, Kuna yi wa matalauta danniya, Kukan umarci mazajenku, Ku ce, “Kawo mini abin sha!”


Kun matsa wa talakawa lamba, Kun ƙwace musu abincinsu. Saboda haka kyawawan gidajen nan da kun gina da dutse, Ba za ku zauna a cikinsu ba, Ba kuwa za ku sha ruwan inabin nan Daga kyawawan gonakin inabinku ba.


Ka kuje kan mayaƙansa da sandunansa, Waɗanda suka zo kamar guguwa don su watsar da mu. Suna murna kamar waɗanda suke zaluntar matalauci a ɓoye.


Kada kuma ku zalunci gwauruwa, wato wadda mijinta ya rasu, da maraya, da baƙo, da matalauci, kada kuma waninku ya shirya wa ɗan'uwansa mugunta a zuciyarsa.


Yesu ya amsa ya ce, “Ni ba mai iska ba ne. Ubana nake girmamawa, ku kuwa wulakanta ni kuke yi.


Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu ibada, masu daraja, da kuma waɗansu manyan gari, suka haddasa tsanani ga Bulus da Barnaba, suka kore su daga ƙasarsu.


Da ba su same su ba, suka jawo Yason da waɗansu 'yan'uwa, har gaban mahukuntan garin, suna ihu suna cewa, “Mutanen nan masu ta da duniya a tsaye, ga su sun zo nan ma,


Amma sa'ad da Galiyo yake muƙaddashin ƙasar Akaya, Yahudawa suka tasar wa Bulus da nufi ɗaya suka kawo shi a gaban shari'a,


Amma Shawulu ya yi ta yi wa Ikkilisiya ɓarna ƙwarai da gaske, yana shiga gida gida, yana jan mata da maza, yana jefa su a kurkuku.


A! Ba ku da gidajen da za ku ci ku sha a ciki ne? Ko kuwa kuna raina Ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma muzanta waɗanda ba su da kome? To, me zan ce muku? Yaba muku zan yi a kan wannan matsala? A'a, ba zan yaba muku ba.


sa'an nan kuka kula da mai tufafi masu ƙawar nan, har kuka ce masa, “Ga mazauni mai kyau a nan,” matalaucin nan kuwa kuka ce masa, “Tsaya daga can,” ko kuwa, “Zauna a nan ƙasa a gabana,”


Ga shi kuwa, zaluncin da kuka yi na hakkin masu girbi a gonakinku yana ta ƙara, kukan masu girbin kuwa ya kai ga kunnen Ubangijin Runduna.


Kun hukunta mai adalci, kun kuma kashe shi, bai kuwa yi muku tsayayya ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan