Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 2:3 - Littafi Mai Tsarki

3 sa'an nan kuka kula da mai tufafi masu ƙawar nan, har kuka ce masa, “Ga mazauni mai kyau a nan,” matalaucin nan kuwa kuka ce masa, “Tsaya daga can,” ko kuwa, “Zauna a nan ƙasa a gabana,”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 in kuka mai da hankali na musamman ga mutumin da yake da riguna masu tsadan nan kuka kuma ce, “Ga wurin zama mai kyau dominka,” amma kuka ce wa matalaucin nan, “Kai tsaya daga can,” ko kuwa, “Ka zauna a ƙasa kusa da ƙafafuna,”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 2:3
8 Iomraidhean Croise  

Matalauci yakan yi roƙo da taushi, maganar matalauci rarrashi ne, amma attajiri yakan yi magana garas.


Sa'an nan su riƙa ce wa sauran mutane, ‘Ku yi nesa da mu gama muna da tsarki da yawa, har da ba za mu taɓa ku ba.’ Ba zan daure da irin waɗannan mutane ba, fushina a kansu kamar wuta ce wadda ba za ta taɓa mutuwa ba.


Sai Hirudus da sojansa suka wulakanta shi, suka yi masa ba'a, da suka sa masa tufafi masu ƙawa kuma, suka mai da shi wurin Bilatus.


Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu, ko da yake shi mawadaci ne, sai ya zama matalauci sabili da ku, domin ta wurin talaucinsa ku wadata.


Misali, in mutum mai zobban zinariya da tufafi masu ƙawa ya halarci taronku, wani matalauci kuma ya shigo a saye da tsummoki,


Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa muku ba? Ba su ne kuwa suke janku zuwa gaban shari'a ba?


Waɗannan su ne masu gunaguni, masu ƙunƙuni, masu biye wa muguwar sha'awa, marubata, masu yi wa mutane bambaɗanci don samun wata fa'ida.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan