Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 2:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Ashe, ba haka kuma Rahab karuwar nan ta sami kuɓuta saboda aikatawarta ba? Wato, sa'ad da ta sauki jakadun nan, ta fitar da su ta wata hanya dabam?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Ta haka kuma ashe, Rahab karuwan nan ba a ɗauke ta mai adalci ce saboda abin da ta yi ba ne sa’ad da ta ba wa ’yan leƙen asirin nan masauƙi ta kuma sallame su suka tafi ta wata hanya dabam?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 2:25
15 Iomraidhean Croise  

Salmon ya haifi Bo'aza (uwa tasa Rahab ce), Bo'aza ya haifi Obida (mahaifiyarsa Rut ce), Obida ya haifi Yesse,


To, wane ne a cikin su biyun ya yi abin da ubansu yake so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah.


har ma Yason ya sauke su! Dukansu kuwa suna saɓa dokokin Kaisar, suna cewa wani ne sarki, wai shi Yesu.”


Ta wurin bangaskiya Rahab karuwar nan ba ta hallaka tare da maƙiya biyayya ba, ta karɓi 'yan ganganimar nan kamar aminai.


To, amma wani zai ce, “Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa sai aikatawa.” To, nuna mini bangaskiya, taka ba tare da aikatawa ba, ni kuma in nuna maka aikatawata, tabbatar bangaskiyata.


Ka gani, ashe, bangaskiyarsa da aikatawarsa duka yi aiki tare, har ta wurin aikatawar nan bangaskiyarsa ta kammala.


Kun ga, ashe, Allah yana kuɓutar da mutum saboda aikatawarsa ne, ba saboda bangaskiya ita kaɗai ba.


Sai Joshuwa ɗan Nun ya aiki mutum biyu 'yan leƙen asirin ƙasa daga Shittim a asirce, ya ce musu, “Tafi, ku leƙo asirin ƙasar, musamman Yariko.” Suka tafi, suka shiga gidan wata mace, karuwa, sunanta Rahab, a nan suka sauka.


Sa'an nan ta zurarar da su da igiya ta taga, gama gidanta yana haɗe da garun birnin ne.


Sai ta ce musu, “Tafi cikin tsaunuka domin kada masu bin sawun su same ku, ku ɓuya a wurin kwana uku, har masu bin sawun su komo, sa'an nan ku kama hanyarku.”


Amma macen ta riga ta ɓoye mutanen nan biyu, sai ta ce, “Gaskiya ce, mutanen sun zo wurina, amma ban san ko daga ina suka zo ba,


Gama ta riga ta kai su bisa rufin ɗaki, ta rufe su da ƙasheshen rama waɗanda ta shimfiɗa a bisa rufin.


Amma birnin da dukan abin da yake cikinsa haram ne ga Ubangiji, sai a hallaka su. Rahab karuwan nan kaɗai ce, da dukan waɗanda suke tare da ita a gidanta za a bari da rai domin ta ɓoye 'yan leƙen asirin ƙasa da muka aika.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan