Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 2:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Aka kuma cika Nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi,” aka kuma kira shi aminin Allah.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Aka kuma cika nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne gare shi,” aka kuma ce da shi abokin Allah.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 2:23
22 Iomraidhean Croise  

Ya amince da Ubangiji, Ubangiji kuwa ya lasafta wannan adalci ne a gare shi.


Ya Allahnmu, kai ne ka kori jama'ar ƙasan nan a gaban jama'arka Isra'ila, ka kuma ba da ita har abada ga zuriya masoyinka Ibrahim.


“Ina so wanda zai yi roƙo ga Allah domina, Kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.


Ta haka Ubangiji ya riƙa yin magana da Musa baki da baki, kamar yadda mutum yakan yi magana da amininsa. Sa'ad da Musa ya koma cikin zango kuma, baransa, Joshuwa, ɗan Num, saurayi, ba zai fita daga cikin alfarwar ba.


“Amma kai, Isra'ila bawana, Kai ne jama'ar da na zaɓa, Zuriyar Ibrahim, abokina,


Ashe, ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba? cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, Shi ne ya zama mafificin dutsen gini.


Suka kuma gicciye 'yan fashi biyu tare da shi, ɗaya dama da shi, ɗaya kuma a hagun.


Sai ya fara ce musu, “Yau Nassin nan ya cika a kunnenku.”


“Ya ku 'yan'uwana, lalle ne a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya faɗa a dā ta bakin Dawuda a game da Yahuza, wanda ya yi wa masu kama Yesu jagaba.


Ko kaɗan, Allah bai juya wa jama'arsa da ya zaɓa tun dā baya ba. Ko ba ku san abin da Nassi ya faɗa ba ne, a game da Iliya? Yadda ya kai kuka ga Allah, a kan Isra'ila, ya ce,


Don a Nassi an ce da Fir'auna, “Na girmama ka ne musamman, domin in nuna ikona a kanka, domin kuma a sanar da sunana a duniya duka.”


Amma Nassi ya kulle kowa a cikin zunubi, don albarkar da aka yi alkawari saboda gaskatawa da Yesu Almasihu, a ba da ita ga masu ba da gaskiya.


Haka ma Ibrahim “ya gaskata Allah, bangaskiyan nan tasa kuma, aka lasafta ta adalci ce a gare shi.”


Kowane Nassi hurarre na Allah ne, mai amfani ne kuma wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma tarbiyyar aikin adalci,


Kun ga, ashe, Allah yana kuɓutar da mutum saboda aikatawarsa ne, ba saboda bangaskiya ita kaɗai ba.


Domin a tabbace yake a Nassi cewa, “Ga shi, na sa mafificin dutsen a gini a Sihiyona, zaɓaɓɓe, ɗaukakakke, Duk mai gaskatawa da shi kuwa, ba zai kunyata ba.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan