Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 2:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Kai marar azanci! Wato sai an nuna maka, bangaskiya ba tare da aikatawa ba, wofiya ce?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Kai wawa, kana son tabbaci cewa bangaskiya marar ayyuka banza ce?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 2:20
16 Iomraidhean Croise  

Manomin da yake aiki ƙwarai yana da isasshen abinci. Wauta ce a ɓatar da lokaci a kan aikin banza.


Ubangiji ya ce, “Wane laifi ne na yi wa kakanninku, Da suka bar bina? Suka bauta wa gumaka marasa amfani, Su kuma suka zama marasa amfani.


Domin kuwa ko da yake sun san da Allah, duk da haka ba su ɗaukaka shi a kan shi Allah ne ba, ba su kuma gode masa ba. Sai tunaninsu ya wofince, zuciyarsu marar fahimta kuma ta duhunta.


Domin mun amince, cewa ta bangaskiya ne mutum yake kuɓuta, ba ta kiyaye ayyukan Shari'a ba.


Ya kai ɗan adam! Wane ne kai har da za ka yi jayayya da Allah? Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa magininsa, “Don me ka yi ni haka?”


In muna a cikin Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.


Kowa ya zaci shi wani abu ne, alhali kuwa shi ba kome ba ne, ya ruɗi kansa ke nan.


Ku lura fa, kada kowa ya ribace ku ta hanyar iliminsa na yaudarar wofi, bisa ga al'adar mutane kawai, wato, bisa ga al'adun duniyar nan, ba bisa ga koyarwar Almasihu ba.


Waɗansu sun kauce wa waɗannan al'amura, har sun bauɗe, sun shiga zancen banza.


Don kuwa akwai kangararrun mutane da yawa, da masu surutan banza, da masu ruɗi, tun ba ma ɗariƙar masu kaciyar nan ba.


In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne.


Haka ma, bangaskiya ita kaɗai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, banza ce.


To, kamar yadda jiki ba numfashi matacce ne, haka ma bangaskiya ba aikatawa matacciya ce.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan