Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 2:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Ka gaskata Allah ɗaya ne? To, madalla. Ai, ko aljannu ma sun gaskata, amma suna rawar jiki don tsoro.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Ka gaskata cewa Allah ɗaya ne. To, da kyau! Ai, ko aljanu ma sun gaskata wannan, har da rawan jiki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 2:19
31 Iomraidhean Croise  

“Ya jama'ar Isra'ila, ku ne shaiduna, Na zaɓe ku al'umma, baiwata, Domin ku san ni, ku gaskata ni, Ku kuma fahimta, ni kaɗai ne Allah. In banda ni ba wani Allah, Ba a taɓa yin wani ba, Ba kuwa za a yi ba.


Ubangiji, wanda yake mulkin Isra'ila, ya kuma fanshe su, Ubangiji Mai Runduna, yake faɗar wannan, “Ni ne farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici, Ba wani Allah sai ni.


Ya jama'ata, kada ku ji tsoro! Kun sani tun daga zamanin dā can, har zuwa yanzu, Na faɗa tun da wuri abin da zai faru. Ku ne kuwa shaiduna! Ko akwai wani Allah? Ko akwai wani Allah mai iko da ban taɓa jin labarinsa ba?”


Na yi wannan domin dukan waɗanda suke daga wannan bangon duniya zuwa wancan Su sani ni ne Ubangiji, Ba kuwa wani Allah sai ni.


Ku tuna da abin da ya faru tuntuni, Ku sani, ni kaɗai ne Allah, Ba kuwa wani mai kama da ni.


Ubangiji kuwa ya amsa ya ce, “Daidai ne ka yi fushi?”


Amma Allah ya ce masa, “Daidai ne ka yi fushi saboda 'yar kurangar?” Yunusa ya amsa, “Hakika, daidai ne a gare ni in yi fushi, har ma in yi fushin da ya isa in mutu!”


A ranar, Ubangiji zai zama Sarkin Duniya duka, zai kuma zama shi ne Ubangiji shi kaɗai, ba wani suna kuma sai nasa.


Sai suka ƙwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai Ɗan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?”


yana cewa, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”


Yesu ya amsa masa ya ce, “Mafi girma shi ne, ‘Ku saurara, ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.


ya ƙwala ihu ya ce, “Ina ruwanka da ni, Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Na gama ka da Allah, kada ka yi mini azaba.”


Sai ya ce musu, “Lalle kun iya yar da umarnin Allah don ku bi al'adunku!


“Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”


Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko.


Sai ta riƙa binmu, mu da Bulus, tana ihu tana cewa, “Mutanen nan fa bayin Allah Maɗaukaki ne, suna kuwa sanar da ku hanyar ceto!”


Amma aljanin ya amsa musu ya ce, “Yesu dai na san shi, na kuma san Bulus, to, ku kuma ku wane ne?”


Bulus yana ba da bayani a kan adalci, da kamunkai, da kuma hukuncin nan mai zuwa, Filikus ya kaɗu, ya kāda baki ya ce, “Yanzu kam, sai ka koma. In na sami zarafi nā kira ka.”


tun da yake Allah ɗaya ne, zai kuwa kuɓutar da masu kaciya ta wurin bangaskiya, marasa kaciya ma ta wannan bangaskiya.


A game da cin abin da aka yanka wa gumaka kuwa, mun sani, duk duniyar nan gunki yana a matsayin abin da babu ne, da kuma, babu wani Allah sai ɗaya.


duk da haka dai, a gare mu kam, Allah ɗaya ne, wato Uba, wanda dukkan abubuwa suke daga gare shi, wanda mu kuma zamansa muke yi, Ubangiji kuma ɗaya ta gare shi muka kasance.


Matsakanci fa ba domin ɗaya ba ne. Amma Allah ɗaya yake.


“Ku ji, ya Isra'ilawa, Ubangiji shi ne Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.


Domin Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya ne, a tsakanin Allah da mutane, Almasihu Yesu, mutum,


Idan lalle kun cika muhimmin umarni yadda Nassi ya ce, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” to, madalla.


Gama waɗansu mutane sun saɗaɗo a cikinku, waɗanda tun zamanin dā aka ƙaddara ga hukuncin nan, marasa bin Allah ne, masu mai da alherin Allah dalilin aikata fajirci, suna kuma ƙin makaɗaicin Ubangijinmu Yesu Almasihu.


Har ma mala'ikun da ba su kiyaye girmansu ba, amma suka bar ainihin mazauninsu, ya tsare su cikin sarƙa madawwamiya a baƙin duhu, har ya zuwa shari'ar babbar ranar nan.


Shi kuwa Ibilis mayaudarinsu, sai da aka jefa shi a tafkin wuta da ƙibiritu, a inda dabbar nan da annabin nan na ƙarya suke, za a kuma gwada musu azaba dare da rana har abada abadin.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan