Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 2:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Misali, in wani ɗan'uwa ko 'yar'uwa suna zaman huntanci, kullum kuma abinci bai wadace su ba,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 A ce wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 2:15
11 Iomraidhean Croise  

idan kuka ƙosar da mayunwata, kuka biya bukatar waɗanda suke shan tsanani, sa'an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu, duhunku kuma zai zama kamar hasken tsakar rana.


Ku ci abincinku tare da mayunwata, ku kuma shigo da matalauta, marasa mahalli a cikin gidajenku. Idan kuma kun ga wanda yake tsirara, ku sa masa sutura, kada kuma ku ɓoye fuskokinku ga 'yan'uwanku.


wanda ba ya cin zalin kowa, wanda yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa, wanda ba ya ƙwace, amma yakan ba mayunwanci abinci, wanda yakan ba huntu tufa,


Kullum kuna tare da gajiyayyu, ko yaushe kuma kuke so, kwa iya yi musu alheri, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba.


Ya amsa musu ya ce, “Duk mai taguwa biyu, ya raba da marar ita, mai abinci ma haka.”


yana wa'azi gabagaɗi da sunan Ubangiji. Ya kuma riƙa magana da Yahudawa masu jin Helenanci, yana muhawwara da su, amma suka yi ta neman kashe shi.


Aka jejeffe su da duwatsu, an gwada su, aka raba su biyu da zarto, aka sare su da takobi. Sun yi yawo saye da buzun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, da ƙunci, da wulakanci.


Ku saurara, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?


Duk kuwa wanda yake da abin hannunsa, yake kuma ganin ɗan'uwansa da rashi, sa'an nan ya rufe ido gare shi, ƙaƙa ƙaunar Allah yake zaune a cikinsa?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan