Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 2:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Gama Shari'a marar jinƙai ce ga wanda ba ya nuna jinƙai. Amma jinƙai yana rinjayar hukunci.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 gama za a yi wa duk wanda bai nuna jinƙai ba hukunci babu jinƙai. Jinƙai yakan yi nasara a kan hukunci!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 2:13
26 Iomraidhean Croise  

Sai suka ce wa junansu, “A ainihin gaskiya, muna da laifi dangane da ɗan'uwanmu, da yake mun ga wahalar da yake sha, sa'ad da kuma ya roƙe mu mu taimake shi, amma ba mu saurara ba, domin haka wannan wahala ta sauko mana.”


Yanzu fa, sai ku saurare ni, ku mayar da kamammun da kuka kwaso daga 'yan'uwanku gama Ubangiji yana fushi da ku ƙwarai.”


Kai, ya Ubangiji, mai aminci ne ga masu aminci, Kai nagari ne, cikakke ga kamilai.


Ƙauna da aminci za su sadu wuri ɗaya, Adalci da salama za su gamu.


Idan ka ƙi jin kukan matalauci, naka kukan da kake yi na neman taimako, ba za a ji ba.


Idan attajirai kake yi wa kyauta, kana kuma zaluntar matalauta don ka arzuta, kai kanka za ka talauce.


Rassan itatuwa sun bushe sun kakkarye, mata kuwa sun tattara, don su riƙa hura wuta da su. Da yake jama'a ba su gane kome ba, Allah Mahaliccinsu ba zai ji tausayinsu ba, ba zai nuna musu jinƙai ba.


Amma bari wanda zai yi fariya, ya yi fariya a kan cewa ya fahimce ni, ya kuma san ni. Ni ne Ubangiji mai yin alheri, da gaskiya, da adalci a duniya, gama ina murna da waɗannan abubuwa, ni Ubangiji na faɗa.”


Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo, ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra'ila?’


Akwai wani Allah kamarka, mai yafe mugunta, Mai kawar da laifin ringin gādonsa? Ba ya riƙon fushi har abada, gama shi mai alheri ne.


“Albarka tā tabbata ga majiya tausayi, domin su ma za a ji tausayinsu.


In kuwa ba ku yafe wa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku naku ba.”


Amma Ibraham ya ce, ‘Ɗana, ka tuna fa, a zamanka na duniya ka sha duniyarka, Li'azaru kuwa ya sha wuya. Amma yanzu daɗi ake ba shi, kai kuwa kana shan azaba.


“Kada ku ɗora wa kowa laifi, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yi wa kowa mugun zato, ku ma ba za a yi muku ba. Ku yafe, ku ma sai a yafe muku.


Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma.


Ga shi kuwa, zaluncin da kuka yi na hakkin masu girbi a gonakinku yana ta ƙara, kukan masu girbin kuwa ya kai ga kunnen Ubangijin Runduna.


Ya kuma ce, “Sarakuna saba'in waɗanda aka yanyanke manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, suka kalaci abincinsu a ƙarƙashin teburina. Allah kuwa ya yi mini kamar yadda na yi musu.” Suka kawo shi Urushalima, a nan ya mutu.


Ya fāɗi a gwiwoyinta, Ya fāɗi ƙasa, yana kwance shiru a ƙafafunta. A ƙafafunta ya sunkuya ya fāɗi, Ya fāɗi matacce har ƙasa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan