Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 2:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Duk wanda yake kiyaye dukkan Shari'a, amma ya saɓa a kan abu guda, ya saɓi Shari'a gaba ɗaya ke nan.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Gama duk wanda ya kiyaye dukan doka amma ya yi tuntuɓe a kan abu ɗaya kaɗai, ya zama mai laifin karya dukansu ke nan.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 2:10
8 Iomraidhean Croise  

Amma sa'ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.


Gama duk waɗanda suke dogara da bin Shari'a la'anannu ne, don a rubuce yake cewa, “Duk wanda bai tsaya ga aikata duk abin da yake rubuce a littafin Shari'a ba, la'ananne ne.”


Ina sāke tabbatar wa duk wanda ya yarda a yi masa kaciya, cewa wajibi ne ya bi dukkan Shari'a.


“ ‘La'ananne ne wanda bai yi na'am da kalmomin dokokin nan don ya yi aiki da su ba.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ ”


Domin dukanmu muna yin kuskure da yawa. In kuwa mutum ba ya shirme a maganarsa, to, shi cikakken mutum ne, yana kuwa iya kame duk sauran gaɓoɓinsa ma.


Saboda haka, ya ku 'yan'uwa, ku ƙara ba da himma ku tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Domin in kun bi waɗannan halaye, ba za ku fādi ba har abada.


Ga wanda yake da iko yă tsare ku daga faɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa aibi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan