Talakawa kamar shaƙar numfashi suke, Manyan mutane, su ma haka suke marasa amfani. Ko an auna su a ma'auni, sam ba su da nauyin kome, Sun fi numfashi shakaf.
Ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi ƙanƙane yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuwa ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ke nan. Ai, wanda yake ƙarami a cikinku shi ne babba.”
In kuwa 'ya'ya muke, ashe, magāda ne kuma, magādan Allah, abokan gādo kuma da Almasihu, in dai har muna shan wuya tare da shi, a kuwa ɗaukaka mu tare da shi.
kamar muna baƙin ciki, kullum kuwa farin ciki muke yi, kamar matalauta muke, duk da haka kuwa muna arzuta mutane da yawa, kamar ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.
“Idan akwai wani danginku matalauci, a wani gari na cikin garuruwan ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, to, kada ku taurara zuciyarku, ku ƙi sakin hannu ga danginku matalauci.
Amma fa, ku lura, kada ku yi tunanin banza a zuciyarku, kuna cewa, ‘Ai, shekara ta bakwai, shekarar yafewa ta yi kusa,’ har ku ɗaure wa danginku matalauci fuska, ku ƙi ba shi kome. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku.
Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.
“ ‘Na san tsananin da kake sha, da talaucinka (amma bisa ga hakika kai mawadaci ne), na kuma san yanken da waɗansu suke yi maka, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, jama'ar Shaiɗan ne.
Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura, Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki. Ya sa su zama abokan 'ya'yan sarki, Ya ɗora su a wurare masu maƙami. Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne, A kansu ya kafa duniya.