Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 1:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Amma fa sai ya roƙa da bangaskiya, ba tare da shakka ba. Don mai shakka kamar raƙuman ruwan teku yake, waɗanda iska take korawa tana tuttunkuɗawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 1:6
14 Iomraidhean Croise  

Kamar ambaliyar ruwa mai fushi kake, Amma ba za ka zama mafi daraja ba, Domin ka hau gadon mahaifinka, Sa'an nan ka ƙazantar da shi.


Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, in kai ne, to, ka umarce ni in zo gare ka a kan ruwan.”


Tashi, ka sauka, ku tafi tare, ba da wata shakka ba, domin ni ne na aiko su.”


An yi wannan kuwa don kada mu sāke zama kamar yara, waɗanda suke jujjuyawa, iskar kowace koyarwa tana ɗaukar hankalinsu, bisa ga wayon mutane da makircinsu da kissoshinsu.


Saboda haka, a kowane wuri ina so maza su yi addu'a, suna ɗaga hannuwa tsarkakakku, ba tare da fushi ko jayayya ba.


Sai mu tsaya da ƙarfi a kan bayyana yarda ga begen nan namu, domin shi mai yin alkawarin nan amintacce ne,


In ba a game da bangaskiya ba kuwa, ba shi yiwuwa a faranta masa rai. Domin duk wanda zai kusaci Allah, lalle ne ya gaskata cewa, akwai shi, yana kuma sakamako ga masu nemansa.


Kada baƙuwar koyarwa iri iri ta bauɗar da ku, ai, abu ne mai kyau alherin Allah ya zamana shi yake ƙarfafa zuciya, ba abinci iri iri ba, waɗanda ba su amfani ga masu dogara da su.


Kada irin mutumin nan mai zuciya biyu, wanda bai tsai da zuciyarsa a gu ɗaya a dukan al'amuransa ba, ya sa rai da wani abu a gun Ubangiji.


Addu'ar bangaskiya kuwa, za ta warkar da marar lafiya Ubangiji kuma zai tashe shi, in ma ya yi zunubi, za a gafarta masa.


Mutanen nan kamar mabubbugen ruwa wadanda suka kafe, ƙasashi ne da iska take kaɗawa. Su ne aka tanada wa matsanancin duhu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan