Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 1:5 - Littafi Mai Tsarki

5 In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 1:5
31 Iomraidhean Croise  

Ubangiji dai ya ba ka basira da haziƙanci domin sa'ad da ya sa ka ka lura da Isra'ila ka kiyaye dokokinsa.


Yanzu sai ka ba ni hikima da sani yadda zan iya kai da kawowa a gaban wannan jama'a, gama wa zai iya mulkin wannan jama'a taka mai yawa haka?”


Amintacciyar zuciya ita kake so, Ka cika tunanina da hikimarka.


Na cika shi da Ruhuna, da hikima, da basira, da ilimi, da fasaha,


Ga shi kuma, ni da kaina, na sa Oholiyab ɗan Ahisamak na kabilar Dan tare da shi, na kuma sa hikima a zukatan masu hikima, don su yi dukan abin da na umarce ka


Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata, Dukan wanda yake nemana kuma zai same ni.


Sai ya fara tsawata wa garuruwan da ya yi yawancin ayyukansa na al'ajabi a cikinsu, don ba su tuba ba.


Daga baya ya bayyana ga sha ɗayan nan, su kansu, sa'ad da suke cin abinci. Sai ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu da taurinkansu, domin ba su gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi ba.


Duk abin da kuka roƙa da sunana kuma zan yi, domin a ɗaukaka Uban ta wurin Ɗan.


In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku.


Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce miki, ‘Sa mini ruwa in sha,’ ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwan rai.”


Ga na ƙarshe ɗin, ƙanshin nan warin mutuwa ne, mai kaiwa ga hallaka, ga na farkon kuwa, ƙanshin rai ne mai kaiwa ga rai. To, wa zai iya ɗaukar nauyin waɗannan abubuwa?


Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.


Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma.


Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske.


Mukan kuma sami duk abin da muka roƙa a gare shi, domin muna bin umarninsa, muna kuma yin abin da yake so.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan