Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 1:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Ya 'yan'uwana ƙaunatattu, ku san wannan, wato, kowa yă yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 ’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 1:19
54 Iomraidhean Croise  

Kowace rana, tun daga rana ta fari zuwa rana ta ƙarshe, Ezra yakan karanta musu daga cikin littafin dokokin Allah. Suka kiyaye idin har kwana bakwai. A rana ta takwas kuma suka muhimmin taro bisa ga ka'ida.


Suka ƙi yin biyayya, Suka manta da dukan abin da ka yi, Suka manta da al'ajaban da ka aikata. Cikin fāriyarsu suka zaɓi shugaba, Don su koma cikin bauta a Masar. Amma kai Allah ne mai gafartawa, Kai mai alheri ne, mai ƙauna, Jinƙanka da girma yake, ba ka yashe su ba.


Sa'ad da suke tsaye a inda suke, sai suka ɗauki kashi ɗaya daga cikin huɗu na yini, suna karanta littafin dokokin Ubangiji Allahnsu. Suka kuma ɗauki kashi ɗaya daga cikin huɗu ɗin na yinin, suna ta hurta laifofi suna kuma yi wa Ubangiji Allahnsu sujada.


Ni kuma sai in tsaya don ba su ce kome ba? Sun tsaya kurum, don ba su da ta cewa?


Bisa ga yawan surutunka, mai yiwuwa ne ƙwarai ka yi zunubi, amma idan kai mai la'akari ne, sai ka yi shiru.


Ka lura da irin abin da kake faɗa don ka kiyaye ranka. Mutumin da bai kula da maganarsa ba, yakan hallakar da kansa.


Mutum mai zafin rai yakan yi aikin wauta, mai mugayen dabaru kuma abin ƙi ne.


Mutum mai kamewa yana da hikima, amma mai zafin rai yana bayyana wautarsa a fili.


Zafin rai yakan kawo jayayya, amma haƙuri yana kawo salama.


Sa'ad da mai hikima ya yi magana yakan sa ilimi ya yi bansha'awa, amma wawaye sukan yi ta sheƙa rashin hankali.


Ya fi kyau ka zama mai haƙuri da ka zama mai ƙarfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.


Mafarin jayayya kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, sai a tsai da ita tun ba ta haɓaka ba.


Mutumin da ya tabbata yana da gaskiya ba zai cika yawan magana ba, natsattsen mutum yana da basira ƙwarai.


Ka saurara kafin ka amsa, idan kuwa ba ka yi ba, ka zama dakiki mai bankunya.


Abin da ka faɗa ya iya cetonka ko ya hallaka ka, saboda haka tilas ne ka karɓi sakamakon maganarka.


Mutum mai hankali yake danne fushinsa. Lokacin da wani ya cuce ka, abin kirki ne, ka yi kamar ba ka kula da shi ba.


Idan mutum mai zafin rai ne, ƙyale shi ya sha sakamakonsa. Idan ka fisshe shi daga cikin wahala sau ɗaya, sai ka sāke yi.


Idan ba ka so ka shiga wahala, ka lura da abin da kake faɗa.


Idan ba ka iya danne fushinka ba, ka zama mai kasala kamar birnin da ba shi da garuka, yana buɗe don a faɗa masa.


Ka ga mutum mai garajen yin magana? To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.


Da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji, sai ta kwanta a ƙafafun Bal'amu. Sai Bal'amu ya husata, ya bugi jakar da sandansa.


Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.


“Dawuda da kansa ya kira shi Ubangiji. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?” Babban taron mutane kuwa sun saurare shi da murna.


Aka kuwa taru maƙil har ba sauran wuri, ko a bakin ƙofa. Shi kuwa yana yi musu wa'azin Maganar Allah.


To, sai duk masu karɓar haraji da masu zunubi suka yi ta matsowa wurinsa su saurare shi.


Suka kuwa rasa abin da za su yi, saboda maganarsa ta ɗauke wa duk jama'a hankali.


To, a kwanakin nan Bitrus ya miƙe tsaye cikin 'yan'uwa, (wajen mutum ɗari da ashirin ne a taron), ya ce,


Nan da nan kuwa na aika maka, ka kuma kyauta da ka zo. To, yanzu ga mu duk mun hallara a gaban Allah, domin mu ji duk irin abin da Ubangiji ya umarce ka.”


Da al'ummai suka ji haka, suka yi farin ciki, suka ɗaukaka Maganar Ubangiji, ɗaukacin kuma waɗanda aka ƙaddara wa samun rai madawwami suka ba da gaskiya.


To, waɗannan Yahudawa kam, sun fi na Tasalonika dattaku, domin sun karɓi Maganar hannu biyu biyu, suna ta nazarin Littattafai kowace rana, su ga ko abin haka yake.


Sai suka himmantu ga koyarwar manzanni da tarayya da juna, da gutsuttsura gurasa, da kuma yin addu'a.


In kun husata, kada ku yi zunubi, kada ma fushinku ya kai faɗuwar rana,


Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da yanke, da kowace irin ƙeta.


Salamar Almasihu kuma tă mallaki zuciyarku, domin lalle ga haka aka kira ku in kuna jiki guda, ku kuma kasance masu gode wa Allah.


Amma yanzu sai ku yar da duk waɗannan ma, wato fushi, da hasala, da ƙeta, da yanke, da alfasha.


Saboda wannan ne kuma muke gode wa Allah ba fasawa, domin sa'ad da kuka karɓi Maganar Allah ta bakinmu, ba ku karɓe ta kamar maganar mutum ce ba, sai dai ainihin yadda take, Maganar Allah, wadda take aiki a cikin zuciyarku, ku masu ba da gasikya.


Kada fa a yaudare ku, ya 'yan'uwana ƙaunatattu.


Ya ku 'yan'uwana, duk sa'ad da gwaje-gwaje iri iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki ƙwarai.


In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne.


Ya ku 'yan'uwana, kada ku nuna bambanci muddin kuna riƙe da bangaskiyarku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangiji Maɗaukaki.


Ku saurara, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?


Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba!


Ya ku 'yan'uwana, kada ku kushe wa juna. Kowa ya kushe wa ɗan'uwansa, ko ya ɗora masa laifi, ya kushe wa shari'a ke nan, ya kuma ɗora mata laifi. In kuwa ka ɗora wa shari'a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne.


Amma fiye da kome, 'yan'uwana, kada ku rantse sam, ko da sama, ko da ƙasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. Sai dai in kun ce “I”, ya tsaya a kan “I” ɗin kawai, in kuwa kun ce “A'a”, ya tsaya a kan “A'a” ɗin kawai, don kada a hukunta ku.


Ya ku 'yan'uwana, in waninku ya bauɗe wa gaskiya, wani kuma ya komo da shi,


Ina rubuto muku, ba don ba ku san gaskiya ba ne, a'a, sai domin kun san ta, kun kuma sani gaskiya ba ta haifar ƙarya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan