Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 1:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 1:17
62 Iomraidhean Croise  

Yusufu ya amsa wa Fir'auna ya ce, “Ba a gare ni ba, Allah zai amsa wa Fir'auna da kyakkyawar amsa.”


Ubangiji dai ya ba ka basira da haziƙanci domin sa'ad da ya sa ka ka lura da Isra'ila ka kiyaye dokokinsa.


Ka kuma ba ɗana Sulemanu cikakkiyar zuciya, har da zai kiyaye umarnanka, da shaidunka, da dokokinka, domin ya aikata su duka, ya kuma gina Haikali wanda na riga na yi tanadi dominsa.”


Amma kai, kana yadda kake kullayaumin, Har abada kake.


Ku yi wa Urushalima addu'ar salama! “Allah ya sa masu ƙaunarki su arzuta!


Shi ne ya halicci rana da wata, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,


Ubangiji shi ne makiyayinmu, sarkinmu mai daraja, Yakan sa mana albarka, da alheri, da daraja, Ba ya hana kowane abu mai kyau ga waɗanda suke aikata abin da yake daidai.


Ubangiji zai arzuta mu, Ƙasarmu kuwa za ta ba da amfanin gona mai yawa.


Ubangiji ne yake ba da hikima. Ilimi da fahimi kuwa suna cikin kalmominsa.


Ya san yadda zai yi aikinsa, gama Allah ya koya masa.


Ni na halicci haske duk da duhu, Ni ne na kawo albarka duk da la'ana. Ni Ubangiji, na yi dukkan waɗannan abu.


Tun da farko na faɗa muku yadda abin zai zama, Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru. Na kuwa ce shirye-shiryena ba za su taɓa fāɗuwa ba, Zan aikata dukan abin da na yi niyyar yi.


“Rana ba za ta ƙara zama haskenki da rana ba, Ko wata ya zama haskenki da dare. Ni, Ubangiji, zan zama madawwamin haskenki, Hasken ɗaukakata zai haskaka a kanki.


“Ni ne Ubangiji, ba na sākewa, domin haka ku zuriyar Yakubu, ba ku ƙāre ɗungum ba.


Ni kuwa zan sauko, in yi magana da kai a can. Zan ɗiba daga cikin ruhun da yake cikinka, in ba su. Su kuma za su ɗauki nawayar jama'ar tare da kai, domin kada ka ɗauki nawayar kai kaɗai.


Sa'an nan Ubangiji ya sauko cikin girgije, ya yi masa magana, ya kuma sa ruhun da yake kansa, ya zama a kan dattawan nan saba'in. Sa'ad da ruhun ya zauna a kansu sai suka yi annabci, amma daga wannan kuma ba su ƙara yi ba.


Allah ba kamar mutum ba ne, da zai yi ƙarya, Ba kuwa ɗan mutum ba ne, da zai tuba. Zai cika dukan abin da ya alkawarta, Ya hurta, ya kuwa cika.


To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?


To, ku da kuke mugaye ma kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama zai ba da Ruhu Mai Tsarki ga masu roƙonsa.”


Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum.


Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Ba mai iya samun kome sai ko an ba shi daga Sama.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.”


Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda yake bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai,”


Da suka ji haka, suka rasa ta cewa, suka kuma ɗaukaka Allah suka ce, “Ashe, har al'ummai ma Allah ya ba su tuba zuwa rai.”


Shi ne Allah ya ɗaukaka ga damansa, Shugaba da kuma Mai Ceto, domin ya buɗe wa Isra'ila hanyar tuba, su kuma sami gafarar zunubansu.


Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.


Wa ya fifita ka da sauran? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? Da yake karɓa ka yi, don me kake fahariya, kamar ba karɓa ka yi ba?


Domin shi Allah wanda ya ce, “Haske yă ɓullo daga duhu ya haskaka,” shi ne ya haskaka zukatanmu domin a haskaka mutane su san ɗaukakarsa a fuskar Yesu Almasihu.


a kuma sa ku ku waye ta idon zuci, domin ku san ko mene ne begen nan da ya kira ku a kai, da kuma ko mene ne yalwar gādonsa mai ɗaukaka a game da tsarkaka,


Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku ba ne, baiwa ce ta Allah,


Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai.


Gama an yi muku alheri, cewa ba gaskatawa da Almasihu kawai za ku yi ba, har ma za ku sha wuya dominsa,


Shi ne kaɗai marar mutuwa, yake kuma zaune a cikin hasken da ba ya kusatuwa. Shi kuwa ba mutumin da ya taɓa ganinsa, ko kuwa zai iya ganinsa. Girma da madawwamin mulki su tabbata a gare shi. Amin, amin.


Yesu Almasihu ba ya sākewa, shi ne a jiya, da yau, hakika har abada ma.


In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.


Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga Sama ba ce, ta duniya ce, ta son zuciya, ta Shaiɗan kuma.


Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma.


Wannan shi ne jawabin da muka ji a gunsa, muke sanar da ku cewa Allah haske ne, ba kuwa duhu gare shi ko kaɗan.


Ta haka ƙauna take, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya aiko Ɗansa, hadayar sulhu saboda a gafarta zunubanmu.


Birnin kuwa ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, domin ɗaukakar Allah ita ce haskensa, Ɗan Ragon kuma fitilarsa.


Ba za a ƙara yin dare ba, ba za su bukaci hasken fitila, ko na rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su, za su kuma sha ni'imar Mulki har abada abadin.


Gama Maɗaukaki na Isra'ila ba zai yi ƙarya, ko ya sāke nufinsa ba. Shi ba mutum ba ne, da zai sāke nufinsa.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan