Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 1:11 - Littafi Mai Tsarki

11 In rana ta tāke da ƙunarta, sai ciyawa ta bushe, hudarta ta kaɗe, kyanta kuma ya gushe. Haka ma mai arziki zai gushe yana a cikin tsakiyar harkarsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Gama in rana ta fito ta yi zafi mai tsanani sai ta sa tsiro yă yanƙwane tsiro; furensa yă kakkaɓe, kyansa kuma yă lalace. Haka ma mai arziki zai shuɗe yayinda yake cikin harkarsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 1:11
27 Iomraidhean Croise  

Zuciyarsu ta karai, Suka fito daga kagararsu suna rawar jiki.


Raina kamar inuwar maraice yake, Kamar busasshiyar ciyawa nake.


An tattake ni kamar busasshiyar ciyarwa, Ba ni da marmarin cin abinci.


Mutum fa, ransa kamar ciyawa ne, Yakan yi girma, ya yi yabanya kamar furen jeji.


Za su shuɗe kamar busasshiyar ciyawa, Za su mutu kamar yadda tsire-tsire suke bushewa.


Bai kuma fi inuwa ba! Duk abin da yake yi banza ne, Yakan tara dukiya, amma bai san wanda zai more ta ba!


Su yi girma har su yi huda, Sa'an nan su yi yaushi su bushe da yamma.


Mukan bar duniyan nan kamar yadda muka shigo ta, ba mu da kome. Dukan ayyukanmu, ba abin da za mu ɗauka mu tafi da shi.


Mulkin Isra'ila ya ƙare, darajarsa tana dushewa kamar rawanin furanni a kan shugabanninsa da suka bugu da giya. Sun bulbula turare a kawunansu na girmankai, amma ga su nan a kwance bugaggu.


Darajan nan mai dushewa ta shugabanni masu girmankai za ta shuɗe kamar 'ya'yan ɓaure, nunan fari, da aka tsinke aka cinye nan da nan da nunarsu.


Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba. Ba za su sha zafin rana da na hamada ba, Gama wanda yake ƙaunarsu ne zai bi da su. Zai bi da su zuwa maɓuɓɓugan ruwa.


Da rana fa ta ɗaga, sai suka yanƙwane, da yake ba su da saiwa sosai, suka bushe.


suna cewa, ‘Na bayan nan, ai, aikin sa'a guda kawai suka yi, ka kuwa daidaita mu, mu da muka yini zubur muna shan wahala da zafin rana.’


To, ga shi, Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!


Da rana fa ta ɗaga, sai suka yanƙwane, da yake ba su da saiwa sosai, suka bushe.


masu moron duniya kuma, kada su ba da ƙarfi ga moronta. Don yayin duniyar nan mai shuɗewa ne.


mu kuma sami gādo marar lalacewa, marar ɓāci, marar ƙarewa kuma, wanda aka keɓe muku a Sama,


Sa'ad da kuma Sarkin Makiyaya ya bayyana, za ku sami kambin ɗaukaka marar dusashewa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan