Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 1:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Daga Yakubu, bawan Allah, da kuma na Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilan nan goma sha biyu da suke a warwatse a duniya. Gaisuwa mai yawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Yaƙub, bawan Allah da kuma na Ubangiji Yesu Kiristi, Zuwa ga kabilan nan goma sha biyu, da suke warwartse a cikin al’ummai. Gaisuwa mai yawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 1:1
41 Iomraidhean Croise  

Ya ɗibi duwatsu goma sha biyu bisa ga yawan kabilan 'ya'yan Yakubu, wanda Ubangiji ya ce masa, “Za a kira sunanka Isra'ila.”


A bikin keɓe Haikalin Allah, suka miƙa bijimai ɗari, da raguna ɗari biyu, da 'yan raguna ɗari huɗu. Suka kuma miƙa hadayu don zunubi saboda dukan Isra'ila, bunsurai goma sha biyu, bisa ga yawan kabilan Isra'ila.


Sa'an nan Haman ya ce wa sarki Ahasurus, “Akwai waɗansu mutane da suke warwatse a jama'ar dukan lardunan mulkinka. Dokokinsu sun sha bambam da na sauran mutane, ba su kuma kiyaye dokokin sarki, don haka ba shi da amfani a wurin sarki ya yi ta haƙuri da su.


Musa kuwa ya rubuta dukan dokokin Ubangiji. Kashegari da sassafe ya gina bagade a gindin dutsen, da kuma ginshiƙai goma sha biyu bisa ga yawan kabilai goma sha biyu na Isra'ila.


A bisa duwatsun nan goma sha biyu, sai a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila bisa ga kabilansu goma sha biyu. Za a zana sunayen kamar hatimi.


An zana sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu a kan duwatsu masu daraja kamar yadda akan yi hatimi.


“Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na watsa su cikin sauran al'umma da cikin ƙasashe.


Zan sa a kawo muku yaƙi a warwatsa ku a baƙin ƙasashe, ƙasarku za ta zama kufai, biranenku kuwa za su lalace.


da Filibus, da Bartalamawas, da Toma, da Matiyu mai karɓar haraji, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza,


Ashe, wannan ba ɗan masassaƙin nan ba ne? Uwa tasa ba sunanta Maryamu ba? 'Yan'uwansa kuwa ba su ne Yakubu, da Yusufu, da Saminu, da kuma Yahuza ba?


Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, a sabon zamani, sa'ad da Ɗan Mutum ya zauna a maɗaukakin kursiyinsa, ku da kuka bi ni, ku ne kuma za ku zauna a kursiyi goma sha biyu, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila.


Sai kuma Andarawas, da Filibus, da Bartalamawas, da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza, da Saminu Bakan'ane,


ku ci ku sha tare da ni a mulkina, ku kuma zauna a kursiyai, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila.


da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Saminu, wanda ake ce da shi Zaloti,


Wanda duk zai bauta mini, ya bi ni. Inda nake kuma, nan bawana zai kasance shi ma. Kowa yake bauta mini, Uba zai girmama shi.”


Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina za shi da har ba za mu same shi ba? Za shi wurin Yahudawan da suka warwatsu a cikin al'ummai ne, ya koya wa al'umman?


Da suka shiga birnin, suka hau soro inda suke zama, wato Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da Andarawas, da Filibus, da Toma, da Bartalamawas, da Matiyu, da Yakubu na Halfa, da Saminu Zaloti, da kuma Yahuza na Yakubu.


Shi kuwa ya ɗaga musu hannu su yi shiru, ya kuma bayyana musu yadda Ubangiji ya fito da shi daga kurkuku. Ya kuma ce, “Ku faɗa wa Yakubu da 'yan'uwa waɗannan abubuwa.” Sa'an nan ya tashi ya tafi wani wuri.


Bayan sun gama jawabi, Yakubu ya amsa ya ce, “Ya ku 'yan'uwa, ku saurare ni.


Domin tun zamanin dā, a kowane gari akwai masu yin wa'azi da littattafan Musa, ana kuma karanta su a majami'u kowace Asabar.”


da wannan takarda cewa, “Daga 'yan'uwanku, manzanni da dattawan Ikkilisiya, zuwa ga 'yan'uwanmu na al'ummai a Antakiya da ƙasar Suriya da ta Kilikiya. Gaisuwa mai yawa.


To, a Urushalima a lokacin, akwai waɗansu Yahudawa masu bautar Allah daga ko'ina cikin ƙasashen duniya.


Kashegari Bulus ya tafi tare da mu wurin Yakubu, dattawan Ikkilisiya kuwa duk suna nan.


“Daga Kalaudiyas Lisiyas zuwa ga mafifici mai mulki Filikus. Gaisuwa mai yawa.


Alkwarin nan kuwa, shi ne wanda kabilanmu goma sha biyu suke himmantuwa ga bauta wa Allah dare da rana, suna sa zuciya su ga cikarsa. Saboda sa zuciyar nan kuma fa Yahudawa suke ƙarata, ya sarki!


Shawulu kuwa yana goyon bayan kisan Istifanas. A ran nan kuwa wani babban tsanani ya auko wa Ikkilisiyar da take Urushalima. Duk aka warwatsa su a lardin Yahudiya da na Samariya, sai dai manzannin kawai.


Daga Bulus, bawan Yesu Almasihu, manzo kirayayye, keɓaɓɓe domin yin bisharar Allah,


Amma ban ga ko ɗaya a cikin sauran manzanni ba, sai dai Yakubu ɗan'uwan Ubangiji.


Don kafin waɗansu su zo daga wurin Yakubu, yakan ci abinci da al'ummai. Amma da suka zo, ya janye jiki ya ware kansa, yana tsoron ɗariƙar masu kaciyar nan.


sai Yakubu da Kefas da Yahaya, su da suke shahararrun ginshiƙan ikkilisiya, da suka ga alherin da Allah ya yi mini, sai suka karɓe mu, ni da Barnaba, hannu biyu biyu, domin mu mu je wurin al'ummai, su kuwa gun masu kaciya.


“Ubangiji zai warwatsa ku cikin dukan al'ummai daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Can za ku bauta wa gumakan itace da na dutse waɗanda ku da kakanninku ba ku san su ba.


sa'an nan Ubangiji Allahnku zai komo da ku daga bauta, ya yi muku jinƙai. Zai tattaro ku daga cikin al'ummai inda ya warwatsa ku.


Na ce, zan watsar da su, in sa a manta da su cikin mutane.


Ubangiji zai warwatsa ku cikin al'ummai. Za ku ragu kaɗan daga cikin al'ummai inda Ubangiji ya warwatsa ku.


Daga Bulus da Timoti, bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan tsarkaka a cikin Almasihu Yesu waɗanda suke a Filibi, tare da masu kula da ikkilisiya da kuma masu hidimarta.


Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo kafin damuna. Aubulus yana gaishe ka, da Budis, da Linas, da Kalaudiya, da kuma dukkan 'yan'uwa.


Daga Bulus, bawan Allah, kuma manzon Yesu Almasihu, saboda bangaskiyar zaɓaɓɓun Allah, da kuma inganta sanin gaskiyar ibadarmu,


Daga Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zaɓaɓɓun Allah da suke bare, a warwatse a Fantas, da Galatiya, da Kafadokiya, da Asiya, da kuma Bitiniya,


Daga Saminu Bitrus, bawan Yesu Almasihu, manzonsa kuma, zuwa ga waɗanda aka yi wa baiwar bangaskiya mai daraja iri ɗaya da tamu, albarkacin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Almasihu.


Daga Yahuza bawan Yesu Almasihu, ɗan'uwan Yakubu zuwa ga kirayayyu, ƙaunatattun Allah Uba, keɓaɓɓu ga Yesu Almasihu.


Sai na ji adadin waɗanda aka buga wa hatimin, dubu ɗari da arba'in da huɗu ne, daga kowace kabilar Isra'ila,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan