Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yahuda 1:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Haka kuma Saduma da Gwamrata, da birane kewayensu, waɗanda su ma suka dulmuya cikin fasikanci da muguwar sha'awa ta jiki, an nuna su domin ishara, suna shan hukuncin madawwamiyar wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yahuda 1:7
27 Iomraidhean Croise  

Mutanen Saduma kuwa mugaye ne masu aikata zunubi ƙwarai gāba da Ubangiji.


Sai kuma Ubangiji ya ce, “Tun da yake kuka a kan Saduma da Gwamrata ya yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni ƙwarai,


Suka kira Lutu suka ce, “Ina mutanen da suka zo wurinka da daren nan? Fito mana da su waje, don mu yi luɗu da su.”


Ya kori dukan karuwai mata da maza da suka ragu a ƙasar a zamanin tsohonsa Asa.


Da a ce Ubangiji Mai Runduna bai rage sauran jama'a ba, da an hallakar da Urushalima gaba ɗaya, kamar yadda aka yi wa Saduma da Gwamrata.


Daular Babila ita ce mafi kyau duka, abin fāriya ce ga jama'arta. Amma ni Ubangiji, zan kaɓantar da ita kamar yadda na yi da Saduma da Gwamrata!


Jama'ar Sihiyona cike da zunubi suke, suna ta rawar jiki don tsoro. Suka ce, “Hukuncin Allah kamar wuta ce mai ci har abada. Akwai wani daga cikinmu da zai iya tsira daga irin wannan wuta?”


Bari wannan mutum ya zama kamar biranen da Ubangiji ya kaɓantar ba tausayi. Bari ya ji kuka da safe, Da rana kuma ya ji gangamin yaƙi,


Abin da ya faru da Saduma da Gwamrata, Da biranen da suke kewaye da su, Shi ne zai faru da Babila. Ba mutumin da zai zauna cikinta.


Gama zunubin mutanena Ya fi zunubin Saduma, Wadda Ubangiji ya hallakar da ita nan da nan.


“Ƙaƙa zan iya rabuwa da ke, ya Ifraimu? Ƙaƙa zan miƙa ki, ya Isra'ila? Ƙaƙa zan maishe ki kamar Adma? Ƙaƙa zan yi da ke kamar Zeboyim? Zuciyata tana motsawa a cikina, Juyayina ya huru.


“Na hallakar da waɗansunku Kamar yadda na hallakar da Saduma da Gwamrata. Kamar sanda kuke, wanda aka fizge daga wuta. Duk da haka ba ku komo wurina ba.


Hakika, ina gaya muku, a Ranar Shari'a za a fi haƙurce wa ƙasar Saduma da ta Gwamrata a kan garin nan.”


Amma ina gaya muku, a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Saduma a kanki.”


Sa'an nan zai ce wa waɗanda suke na hagun, ‘Ku rabu da ni, la'anannu, ku shiga madawwamiyar wuta, wadda aka tanadar wa Iblis da mala'ikunsa.


amma a ranar da Lutu ya fita daga Saduma, aka zubo wuta da duwatsun wuta daga sama, aka hallaka su duka.


Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo,


Dukan ƙasa za ta zama kibritu da gishiri, ba shuka, ba amfani, ciyawa kuma ba ta tsirowa, kamar yadda Ubangiji ya kabantar da Saduma da Gwamrata, da Adam da Zeboyim, da zafin fushinsa.


yă kuma ba ku hutu har da mu ma, ku da ake ƙuntata wa ɗin, a ranar bayyanar Ubangiji Yesu daga Sama tare da manyan mala'ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa,


yana ta sāka wa waɗanda suke ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suka ƙi bin bisharar Ubangijinmu Yesu.


Da yawa kuwa za su bi fajircinsu, har za a kushe hanyar gaskiya saboda su.


da yake kuma ya mai da biranen Saduma da Gwamrata toka, ya yi musu hukuncin hallaka, ya mai da su abin ishara ga marasa bin Allah,


Ta maganar Allah ne kuma sama da ƙasa da suke a nan a yanzu, aka tanada su ga wuta, ana ajiye su, har ya zuwa ranar nan da za a yi wa marasa bin Allah shari'a, a hallaka su.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan