Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yahuda 1:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Har ma mala'ikun da ba su kiyaye girmansu ba, amma suka bar ainihin mazauninsu, ya tsare su cikin sarƙa madawwamiya a baƙin duhu, har ya zuwa shari'ar babbar ranar nan.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yahuda 1:6
12 Iomraidhean Croise  

Hakika, ina gaya muku, a Ranar Shari'a za a fi haƙurce wa ƙasar Saduma da ta Gwamrata a kan garin nan.”


Sa'an nan zai ce wa waɗanda suke na hagun, ‘Ku rabu da ni, la'anannu, ku shiga madawwamiyar wuta, wadda aka tanadar wa Iblis da mala'ikunsa.


Sai suka ƙwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai Ɗan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?”


Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa'ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.


Amma ga shi, saboda ƙeƙasasshiyar zuciyarka marar tuba, kana nema wa kanka fushin Allah a ranar fushi, sa'ad da za a bayyana hukuncin Allah macancani.


Ai, famarmu ba da 'yan adam muke yi ba, amma da mugayen ruhohi ne na sararin sama, masarauta, masu iko, da waɗanda ragamar mulkin zamanin nan mai duhu take hannunsu.


sai dai matsananciyar fargabar hukunci, da kuma wuta mai tsananin zafi, wadda za ta cinye maƙiyan Allah.


Da yake Allah bai rangwanta wa mala'iku ba sa'ad da suka yi zunubi, sai ya jefa su a Gidan Wuta, ya tura su a cikin ramummuka masu zurfi, masu baƙin duhu, a tsare su har ya zuwa ranar hukunci,


ashe kuwa, Ubangiji ya san yadda zai kuɓutar da masu tsoronsa daga gwaje-gwaje, ya kuma tsare marasa adalci a kan jiran hukunci, har ya zuwa ranar shari'a,


Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu kai da kawowa, waɗanda aka tanada wa matsanancin duhu har abada.


Shi kuwa Ibilis mayaudarinsu, sai da aka jefa shi a tafkin wuta da ƙibiritu, a inda dabbar nan da annabin nan na ƙarya suke, za a kuma gwada musu azaba dare da rana har abada abadin.


Sai ya kama macijin nan, wato, macijin nan na tun dā dā, wanda yake shi ne Ibilis, shi ne kuma Shaiɗan, ya ɗaure shi har shekara dubu,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan