Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yahuda 1:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ya ku ƙaunatattuna, da yake dā ma ina ɗokin rubuto muku zancen ceton nan namu, mu duka, sai na ga wajibi ne in rubuto muku in gargaɗe ku, ku dage ƙwarai a kan bangaskiyar nan da aka danƙa wa tsarkaka sau ɗaya tak, ba ƙari.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Abokaina ƙaunatattu, ko da yake na yi marmari ƙwarai in rubuta muku game da ceton nan namu, sai na ga ya dace in rubuta, in gargaɗe ku ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya wadda aka danƙa wa mutane masu tsarki na Allah sau ɗaya tak.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yahuda 1:3
44 Iomraidhean Croise  

Sai na yi musu faɗa na la'ance su, na bugi waɗansu daga cikinsu, na ciccire gashin kansu, na sa su rantse da Allah, cewa ba za su aurar da 'ya'yansu mata ga 'ya'yan maza na bare ba, ko kuma su auro wa 'ya'yansu maza 'yan matan bare, ko su auro wa kansu.


Amma Ubangiji ya ceci Isra'ila, Nasararsa kuwa za ta tabbata har abada, Mutanensa ba za su taɓa shan kunya ba.


“Ku juyo wurina a cece ku, Ku mutane ko'ina a duniya! Ni kaɗai ne Allah da yake akwai.


Ubangiji ya ce, “Sun tanƙwasa harshensu kamar baka, Ƙarya ce take rinjayar gaskiya a ƙasar. Suna ta cin gaba da aikata mugunta, Ba su kuwa san ni ba.


yana yi musu bayani, yana kuma tabbatarwa, cewa lalle ne, Almasihu yă sha wuya, ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Yesun nan da nake sanar muku, shi ne Almasihu.”


don yā kayar da Yahudawa ƙwarai a gaban jama'a, yana tabbatar musu ta wurin Littattafai cewa Almasihu dai Yesu ne.


domin ban ji nauyin sanar da ku dukan nufin Allah ba.


To, sai ku sani, wannan ceto na Allah, an aiko da shi har ga al'ummai, su kam za su saurara.”


Ba kuma samun ceto ga wani, domin ba wani suna duk duniyan nan da aka bayar cikin mutane, wanda lalle ta wurinsa ne za mu sami ceto.”


Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka take yi, yawan masu bi kuma a birnin Urushalima sai ta ƙaruwa yake yi ƙwarai da gaske, firistoci masu yawan gaske kuma suka yi na'am da bangaskiyar nan.


Amma Hananiya ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, na sha jin labarin mutumin nan gun mutane da yawa, kan yawan muguntar da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima.


Sai Shawulu ya ƙara ƙarfafa, yana ta dama hankalin Yahudawan da suke zaune a Dimashƙu, yana tabbatarwa, cewa Yesu shi ne Almasihu.


Jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, shi ne wanda na karɓo, cewa, Almasihu ya mutu domin zunubanmu, kamar yadda Littattafai suka faɗa,


Amma ko kaɗan ba mu sakar musu ba, ko da taƙi, domin gaskiyar bishara tă zaune muku.


Ba sauran cewa Bayahude ko Ba'al'umme, ko ɗa, ko bawa, ko namiji ko mace. Ai, dukkanku ɗaya kuke, na Almasihu Yesu.


Ku dubi irin rubutu gwada-gwada da nake muku da hannuna!


Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, zuwa ga mutanensa tsarkaka da suke a Afisa, amintattu a cikin Almasihu Yesu.


Ta haka za ku kawar da alhakin jinin marar laifi daga cikinku, sa'ad da kuka yi abin da yake daidai a wurin Ubangiji.”


Ubangiji kuwa ya ba ni allunan nan biyu na dutse da shi kansa ya rubuta. A kansu aka rubuta maganar da Ubangiji ya yi muku daga bisa dutsen a tsakiyar wuta a ranar taron.


Daga Bulus da Timoti, bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan tsarkaka a cikin Almasihu Yesu waɗanda suke a Filibi, tare da masu kula da ikkilisiya da kuma masu hidimarta.


Sai dai ku yi zaman da ya cancanci bisharar Almasihu, domin ko na zo na gan ku, ko kuwa ba na nan, in ji labarinku, cewa kun dage, nufinku ɗaya, ra'ayinku ɗaya, kuna fama tare saboda bangaskiyar da bishara take sawa,


zuwa ga tsarkaka da amintattun 'yan'uwa cikin Almasihu da suke a Kolosi. Alheri da salamar Allah Ubanmu su tabbata a gare ku.


Amma ko da yake dā ma can mun sha wuya, an kuma wulakanta mu a Filibi, kamar yadda kuka sani, duk da haka da taimakon Allahnmu muka sanar da ku bisharar Allah gabagaɗi, amma sai da matsanancin fama.


Na danƙa maka wannan umarni, ya ɗana Timoti, bisa ga annabce-annabcen da dā aka faɗa a kanka, domin ka ƙarfafu ta wurinsu, ka yi yaƙi mai kyau,


Ka yi fama, famar gaske saboda bangaskiya, ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira ka saboda shi, sa'ad da ka bayyana yarda, kyakkyawar bayyana yarda, a gaban shaidu masu yawa.


Ka yi koyi da sahihiyar maganar da ka ji daga gare ni, da bangaskiya da ƙauna da take ga Almasihu Yesu.


zuwa ga Titus, ɗana na hakika ta wajen bangaskiyarmu mu duka. Alheri da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Mai Cetonmu su tabbata a gare ka.


To, ina roƙonku, 'yan'uwa, ku yi haƙuri da gargaɗina, don taƙaice na rubuto muku.


Ko da yake mun faɗi haka, a game da ku kam, ya ƙaunatattu, mun tabbata kuna a kan abubuwa mafiya kyau na zancen ceto.


Na rubuto muku wasiƙar nan a taƙaice ta hannun Sila, ɗan'uwa mai aminci, a yadda na ɗauke shi, domin in yi muku gargaɗi, in kuma sanar da ku, cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske, ku tsaya a gare shi da ƙarfi.


Daga Saminu Bitrus, bawan Yesu Almasihu, manzonsa kuma, zuwa ga waɗanda aka yi wa baiwar bangaskiya mai daraja iri ɗaya da tamu, albarkacin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Almasihu.


Da ba su taɓa sanin hanyar adalci tun da fari ba, da ya fiye musu, bayan sun san ta, sa'an nan su juya ga barin umarnin nan mai tsarki.


Daga Yahuza bawan Yesu Almasihu, ɗan'uwan Yakubu zuwa ga kirayayyu, ƙaunatattun Allah Uba, keɓaɓɓu ga Yesu Almasihu.


Ya ku ƙaunatattuna, lalle ku tuna da maganar da manzannin Ubangijinmu Yesu Almasihu suka faɗa a dā,


Amma ya ku ƙaunatattuna, ku riƙa inganta kanku ga bangaskiyarku mafi tsarki, kuna addu'a da ikon Ruhu Mai Tsarki.


Sun kuwa yi nasara da shi albarkacin jinin Ɗan Ragon nan, da kuma albarkacin maganar da suka shaida, domin ba su yi tattalin ransu ba, har abin ya kai su ga kisa.


Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan