Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yahuda 1:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Waɗannan su ne masu gunaguni, masu ƙunƙuni, masu biye wa muguwar sha'awa, marubata, masu yi wa mutane bambaɗanci don samun wata fa'ida.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Waɗannan mutane dai, gunaguni gare su, kullum ganin laifin waɗansu suke yi. Muguwar sha’awa ce kaɗai tunaninsu. Sun cika da banzar magana ta yabon kansu. Suna ruɗin mutane da zaƙin baki don samun ribar kansu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yahuda 1:16
38 Iomraidhean Croise  

Ba zan yi wa kowa son zuciya ba, Ko kuma in yi wa wani fādanci.


Ba ya nuna sonkai ga sarakuna, Ko kuma ya fi kulawa da attajira fiye da matalauta, Gama shi ya halicce su duka.


Suka zauna cikin alfarwansu suna ta gunaguni, Sun ƙi su saurari Ubangiji.


Yakan raina waɗanda Allah ya ƙi su, Amma yana girmama waɗanda suke yi wa Ubangiji biyayya, Kullum yana cika alkawaran da ya yi ko ta halin ƙaƙa,


Ba su jin tausayi, suna magana da girmankai,


Sukan yi wa waɗansu ba'a, Suna faɗar mugayen abubuwa, Masu girmankai ne su, suna shawara A kan yadda za su zalunci waɗansu.


Nuna sonkai mugun abu ne, waɗansu alƙalai sukan aikata mugunta saboda 'yar ƙaramar rashawa.


Wawaye za su koya su gane, waɗanda a kullum sai gunaguni suke yi, za su yi murna su koya.”


“Ku yi gaskiya da adalci cikin shari'a, kada ku ma ku yi wa matalauci son zuciya, ko ku goyi bayan mawadaci.


Mutanen da Musa ya aika su leƙo asirin ƙasar, waɗanda suka komo, suka sa taron jama'a su yi gunaguni a kansa saboda sun kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar,


Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji!”


Kashegari dukan taron Isra'ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suna cewa, “Ku ne sanadin mutuwar jama'ar Ubangiji.”


Sai Farisiyawa da malaman Attaura suka riƙa gunaguni suna cewa, “Haba! Wannan mutum yana karɓar masu zunubi, har ma tare suke cin abinci!”


Da suka ga haka, duk suka yi ta gunaguni, suka ce, “A! A gidan mai zunubi dai ya sauka!”


Sai Farisiyawa da malamansu na Attaura suka yi wa almajiransa gunaguni suka ce, “Don me kuke ci kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”


Sai fa Yahudawa suka yi masa gunaguni, domin ya ce, “Ni ne Gurasan da ya sauko daga Sama.”


Yesu kuwa, da yake ya sani a ransa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce musu, “Wato, wannan ne ya zamar muku abin tuntuɓe?


Kada kuma mu yi gunaguni yadda waɗansu suka yi, har mai hallakarwa ya hallaka su.


Maganata ita ce, ku yi zaman Ruhu, ba kuwa za ku biye wa halin mutuntaka ba.


Waɗanda kuwa suke su na Almasihu Yesu ne, sun gicciye halin mutuntaka da mugayen sha'awace-sha'awace iri iri.


Sai kuka yi ta gunaguni cikin alfarwanku, kuna cewa, ‘Ai, saboda Ubangiji ya ƙi mu, shi ya sa ya fisshe mu daga ƙasar Masar, don ya bashe mu a hannun Amoriyawa, su hallaka mu.


Kome za ku yi, kada ku yi da gunaguni, ko gardama,


ba ta muguwar sha'awa ba, yadda al'ummai suke yi, waɗanda ba su san Allah ba.


da kuma yawan tankiya a cikin mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda har gaskiya ta ƙaurace musu, suna tsammani bin Allah hanya ce ta samu.


Don lokaci zai zo da mutane ba za su jure sahihiyar koyarwa ba, amma saboda kunnensu yana ƙaiƙayi, sai su taro masu koyarwa da za su biya musu muradinsu.


Ku yi zaman 'ya'ya masu biyayya. Kada ku biye wa muguwar sha'awarku ta dā, ta lokacin jahilcinku.


Ya ƙaunatattuna, ina roƙonku don ku baƙi ne, bare kuma, ku guje wa mugayen sha'awace-sha'awace na halin mutuntaka waɗanda suke yaƙi da zuciyarku.


domin a nan gaba yă ƙarasa sauran zamansa na jiki ba tare da biye wa muguwar sha'awar zuciya ba, sai dai nufin Allah.


tun ba waɗanda suka dulmuya a cikin muguwar sha'awa mai ƙazantarwa ba, suke kuma raina mulki. Masu tsaurin ido ne su, masu taurin kai kuma, ba sa jin tsoron zagin masu ɗaukaka.


Ta surutai barkatai marasa kan gado na ruba, da halinsu na fasikanci sukan shammaci waɗanda da ƙyar suke kuɓucewa daga masu zaman saɓo,


Da farko dai lalle ne ku fahimci wannan, cewa a can zamanin ƙarshe masu ba'a za su zo suna ba'a, suna biye wa muguwar sha'awarsu,


don ya zartar da hukunci kan kowa, yă kuma tabbatar wa marasa bin Allah dukan aikinsu na rashin bin Allah, da suka aikata ta hanyar rashin bin Allah, da kuma baƙaƙen maganganu da masu zunubi marasa bin Allah suka yi game da shi.”


da suka ce da ku, “A zamanin ƙarshe za a yi waɗansu mutane masu ba'a, masu biye wa muguwar sha'awarsu ta rashin bin Allah.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan