Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yahuda 1:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu kai da kawowa, waɗanda aka tanada wa matsanancin duhu har abada.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yahuda 1:13
12 Iomraidhean Croise  

Kakan kwantar da rurin tekuna, Kakan kwantar da rurin igiyar ruwa, Kakan kwantar da tarzomar jama'a.


Amma mugaye suna kama da tumbatsar teku, gama ba ta iya natsuwa. Ruwanta kuma yana tumbatsa, ya gurɓace, ya ƙazantu.”


Ƙarshensu hallaka ne, Allahnsu ciki ne, rashin kunyarsu ita ce abar taƙamarsu, sun ƙwallafa ransu a kan al'amuran duniya.


Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu.


Mutanen nan kamar mabubbugen ruwa wadanda suka kafe, ƙasashi ne da iska take kaɗawa. Su ne aka tanada wa matsanancin duhu.


Har ma mala'ikun da ba su kiyaye girmansu ba, amma suka bar ainihin mazauninsu, ya tsare su cikin sarƙa madawwamiya a baƙin duhu, har ya zuwa shari'ar babbar ranar nan.


Shi kuwa Ibilis mayaudarinsu, sai da aka jefa shi a tafkin wuta da ƙibiritu, a inda dabbar nan da annabin nan na ƙarya suke, za a kuma gwada musu azaba dare da rana har abada abadin.


Amma matsorata, da marasa riƙon amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibiritu, wanda yake shi ne mutuwa ta biyu.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan