Rut 4:4 - Littafi Mai Tsarki4 Don haka na ga ya kamata in sanar da kai cewa, ka saye ta a gaban waɗanda suke zaune a nan, da a gaban dattawan jama'a. Idan za ka fanshi gonar sai ka fanshe ta, idan kuwa ba za ka fansa ba, ka faɗa mini don in sani, gama daga kai sai ni muke da izinin fansar gonar.” Sai mutumin ya ce, “Zan fanshe ta.” Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20204 Na ga ya kamata in jawo hankalinka ga batun in kuma ba da shawara ka saye shi a gaban waɗannan da suke zazzaune a nan da kuma a gaban dattawan jama’a. In kana so ka fanshe shi, to, sai ka yi. Amma in ba za ka yi ba, sai ka faɗa mini, don in sani. Gama babu wani mai izinin yin haka sai kai, ni ne kuwa na biye.” Sai ya ce, “Zan fansa.” Faic an caibideil |