Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 4:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Sai mata suka ce wa Na'omi, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, da bai bar ki bā dangi na kusa ba, Allah ya sa ɗan ya yi suna a cikin Isra'ila.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Mata suka ce wa Na’omi, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda a wannan rana bai bar ki ba tare da dangi mai fansa ba. Allah yă sa yă zama sananne a dukan Isra’ila!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 4:14
13 Iomraidhean Croise  

Zan kuwa maishe ka al'umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka.


ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa ga maigidana ba. Ubangiji ya bi da ni har zuwa gidan ɗan'uwan maigidana.”


Har yanzu kuwa ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta raɗa masa suna Yahuza. Daga nan sai ta daina haihuwa.


Sai maƙwabta da 'yan'uwanta suka ji yadda Ubangiji ya ji ƙanta ƙwarai, har suka taya ta farin ciki.


Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka.


Ta haka, in wata gaɓa ta ji ciwo, duk sai su ji ciwo tare, in kuwa an yabi wata, duk sai su yi farin ciki tare.


Ku godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu.


Lalle ne a kullum mu gode wa Allah saboda ku, 'yan'uwa, haka kuwa ya kyautu, da yake bangaskiyarku haɓaka take yi ƙwarai da gaske, har ma ƙaunar kowane ɗayanku ga juna ƙaruwa take yi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan