Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 4:12 - Littafi Mai Tsarki

12 gidanku kuma ya zama kamar gidan Feresa, wanda Tamar ta haifa wa Yahuza, saboda 'ya'yan da Ubangiji zai ba ka ta wurin wannan mace.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Ta wurin ’ya’yan da Ubangiji zai ba ka ta wurin wannan mace, bari iyalinka yă zama kamar na Ferez, wanda Tamar ta haifa wa Yahuda.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 4:12
8 Iomraidhean Croise  

Amma da ya janye hannunsa, ga ɗan'uwansa ya fito, sai ta ce, “A'a, ta haka za ka keta ka fito!” Saboda haka aka raɗa masa suna Feresa.


'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan'ana). 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.


Surukarsa Tamar, matar ɗansa kuma ta haifa masa Feresa da Zera. Yahuza yana da 'ya'ya maza biyar.


Ashe, ba kai da ita Allah ya maishe ku jiki ɗaya da ruhu ɗaya ba? Me Allah yake nufi da wannan? Yana so 'ya'yanmu su zama 'yan halal masu tsoron Allah. Domin haka ku kula fa, kada kowa ya ci amanar matarsa ta ƙuruciya.


Yahuza kuwa ya haifi Feresa da Zera (uwa tasu Tamar ce), Feresa ya haifi Hesruna, Hesruna ya haifi Aram,


Wannan shi ne asalin zuriyar Dawuda. Aka fara daga Feresa zuwa Dawuda. Feresa ne mahaifin Hesruna, Hesruna kuma ya haifi Arama, Arama ya haifi Amminadab, Amminadab kuma ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon, Salmon kuma ya haifi Bo'aza, Bo'aza ya haifi Obida, Obida kuma ya haifi Yesse, sa'an nan Yesse ya haifi Dawuda.


Eli kuwa yakan sa wa Elkana da matarsa albarka, ya ce, “Ubangiji ya ba ka waɗansu 'ya'ya ta wurin matan nan a maimakon wanda kuka ba Ubangiji.” Bayan wannan sai su koma gida.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan