Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 4:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Dukan jama'a suka ce, “Mu ne shaidu, Ubangiji yă sa matar da za ta zo gidanka ta zama kamar Rahila da Lai'atu waɗanda suka gina gidan Isra'ila. Allah ya arzuta ka cikin Efrata, yă sa ka yi suna a cikin Baitalami,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Sai dattawan da kuma dukan waɗanda suke a ƙofar suka ce, “Mu shaidu ne. Bari Ubangiji yă sa macen da take zuwa cikin gidanka ta zama kamar Rahila da Liyatu, waɗanda tare suka gina gidan Isra’ila. Bari ka sami martaba a cikin Efrata ka kuma zama sananne cikin Betlehem.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 4:11
24 Iomraidhean Croise  

A sa'an nan Efron yana tare da Hittiyawa. Sai Efron Bahitte ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan Hittiyawa, da gaban dukan waɗanda suke shiga ta ƙofar birninsa, ya ce,


Suka sa wa Rifkatu albarka, suka ce mata, “'Yar'uwarmu, ki zama mahaifiyar dubbai, Har dubbai goma, Bari zuriyarki kuma su gāji ƙofofin maƙiyansu!”


Laban dai yana da 'ya'ya mata biyu, sunan babbar Lai'atu, sunan ƙaramar kuwa Rahila.


Da gari ya waye kuma ga shi, ashe, Lai'atu ce. Sai Yakubu ya ce wa Laban, “Mene ne wannan da ka yi mini? Ba don Rahila na yi maka barantaka ba? Don me ka yaudare ni?”


Lai'atu fa ta yi ciki ta haifi ɗa, ta raɗa masa suna Ra'ubainu, gama ta ce, “Saboda Ubangiji ya dubi wahalata, hakika, yanzu mijina zai ƙaunace ni.”


'Ya'yan Lai'atu, su ne Ra'ubainu ɗan farin Yakubu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza, da Issaka, da Zabaluna.


'Ya'yan Rahila, su ne Yusufu da Biliyaminu.


Sa'an nan ta rubuta wasiƙu da sunan Ahab, ta hatimce su da hatiminsa, sa'an nan ta aika da wasiƙun zuwa ga dattawa da fādawan da suke zaune a birnin tare da Nabot.


da Salma, shi kuwa ya kafa Baitalami, da Haref ɗansa kuma wanda ya kafa Bet-gader.


Mun ji labari akwatin alkawari yana Baitalami, Amma muka same shi a kurmi.


Hikimar mata takan gina gidaje, amma wauta takan rushe su.


Mijinta sananne ne a dandali, sa'ad da yake zaune tare da dattawan gari.


Na sa hannu a takarda, na buga hatimi na liƙe, na sami shaidu na kuwa auna kuɗin da ma'auni.


“Baitalami cikin Efrata, Wadda kike 'yar ƙarama a cikin kabilar Yahuza, Amma daga cikinki wani zai fito wanda zai sarauci Isra'ila Wanda asalinsa tun fil azal ne.”


“ ‘Ke ma Baitalami, ta kasar Yahuza, Ko kusa ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin manyan garuruwan Yahuza ba, Domin daga cikinki za a haifi wani mai mulki, Wanda zai zama makiyayin jama'ata, Isra'ila.’ ”


Amma idan mutum ya ƙi ya auri matar ɗan'uwansa, marigayi, sai matar ta tafi wurin dattawa a dandalin ƙofar gari, ta ce, ‘Ɗan'uwan mijina, marigayi, ya ƙi wanzar da sunan ɗan'uwansa cikin Isra'ila, gama ya ƙi yi mini abin da ya kamaci ɗan'uwan marigayi, ya yi.’


sai matar ɗan'uwansa, marigayi, ta tafi wurinsa a gaban dattawan, ta kwaɓe takalmin ƙafarsa, ta tofa masa yau a fuskarsa, ta ce, ‘Haka za a yi wa wanda ya ƙi kafa gidan ɗan'uwansa.’


Sunan mutumin, Elimelek, matarsa kuwa Na'omi, 'ya'yanta maza kuma Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Baitalami ta Yahudiya. Suka tafi Mowab suka zauna a can.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan