Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 3:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Ya ce, “Wace ce?” Sai ta amsa, “Ni ce Rut, baranyarka, sai ka rufe ni da mayafinka, gama kai dangi ne na kusa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Sai ya yi tambaya ya ce, “Ke wace ce?” Ta amsa ta ce, “Ni ce baranyarka Rut, ka rufe ni ta mayafinka da yake kai dangi, mai fansa ne na kusa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 3:9
10 Iomraidhean Croise  

“Sa'ad da na sāke wucewa kusa da ke, na dube ki, ga shi, kin kai lokacin da za a ƙaunace ki, sai na yafe miki tufata, na rufe tsiraincinki, na rantse miki, na ƙulla alkawari da ke, kin kuwa zama tawa, ni Ubangiji Allah na faɗa.


Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”


Na'omi ta ce wa Rut, “Ubangiji wanda bai daina nuna alheri ga masu rai da marigayan ba, ya sa masa albarka.” Ta ƙara da cewa, “Ai, mutumin, shi danginmu ne na kusa.”


Sa'an nan ya ce, “Ubangiji ya sa miki albarka 'yata, yanzu kin nuna alheri mafi girma fiye da na dā da yake ba ki nemi saurayi, matalauci ko attajiri ba.


Gaskiya ce, ni dangi na kusa ne, amma akwai wanda yake dangi na kusa fiye da ni.


Da tsakar dare, sai mutumin ya farka a firgice, ya juya, sai ga mace kwance a wajen ƙafafunsa.


Don haka na ga ya kamata in sanar da kai cewa, ka saye ta a gaban waɗanda suke zaune a nan, da a gaban dattawan jama'a. Idan za ka fanshi gonar sai ka fanshe ta, idan kuwa ba za ka fansa ba, ka faɗa mini don in sani, gama daga kai sai ni muke da izinin fansar gonar.” Sai mutumin ya ce, “Zan fanshe ta.”


Sai dangin nan mafi kusa ya ce, “Ba zan iya ɗaukar Rut ba, domin kada in ɓata nawa gādo. Na bar maka ka ɗauke ta gama ni ba zan iya ba.”


Sai ta rusuna har ƙasa, ta ce, “Ni baranyarsa ce, ina a shirye in wanke ƙafafun barorinsa.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan