Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 3:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Sa'ad da Bo'aza ya ci ya sha yana cikin jin daɗi, sai ya je ya kwanta kusa da tsibin tsabar sha'ir. Sa'an nan Rut ta tafi a hankali, ta buɗe mayafin da ya rufa da shi wajen ƙafafunsa, ta kwanta a ciki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Sa’ad da Bowaz ya gama ci da sha yana kuma cikin farin ciki, sai ya tafi ya kwanta a ƙarshen tarin hatsi. Rut kuwa ta sulalle ta je ta buɗe ƙafafunsa ta kwanta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 3:7
18 Iomraidhean Croise  

Daga teburin da yake a gabansa aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Biliyaminu ya yi biyar ɗin na kowannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.


Absalom ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku lura sa'ad da Amnon ya bugu da ruwan inabi, in na ce, ‘Bugi Amnon’, sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro, gama ni na umarce ku, sai dai ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka.”


Yezebel, matarsa, ta ce masa, “Ba kai ne kake mulkin Isra'ila ba? Tashi, ka ci abinci, ka yi farin ciki, zan ba ka gonar inabin Nabot Bayezreyele.”


A rana ta bakwai sa'ad da zuciyar sarki take murna saboda ruwan inabi, sai ya umarta bābāninsa guda bakwai, waɗanda suke yi masa hidima, wato Mehuman, da Bizta, da Harbona, da Bigta, da Abagta, da Zetar, da Karkas,


Don ya yi ruwan inabin da zai sa shi farin ciki, Ya sami man zaitun wanda zai sa shi fara'a, Da abincin da zai ba shi ƙarfi.


Akan shirya abinci don jin daɗi, ruwan inabi kuwa don faranta zuciya, amma ba za ka sami ko ɗaya ba, sai idan kana da kuɗi.


Ba abin da ya fi wa mutum kyau fiye da ya ci, ya sha, ya saki jiki, ya ci moriyar aikinsa. Na gane wannan ma daga wurin Allah ne.


Abin da na ce, shi ne mutum ya ji daɗi, domin iyakar jin daɗinsa a wannan rai, shi ne ya ci, ya sha, ya ji wa kansa daɗi. Aƙalla yana iya yin wannan in ya yi aiki a kwanakinsa wanda Allah ya ba shi a wannan duniya.


Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da fara'a, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah.


To, duk abin da kuke yi, ko ci, ko sha, ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.


Kada kuma ku bugu da giya, hanyar masha'a ke nan. Sai dai ku cika da Ruhu,


Sa'ad da suke ta farin ciki, sai suka ce, “A kawo Samson ya yi mana wasa.” Sai suka kawo Samson daga kurkuku, ya kuwa yi wasa a gabansu. Suka sa ya tsaya a tsakanin ginshiƙai.


Sa'ad da suke cikin jin daɗin ci da sha, 'yan iskan da suke birnin suka zo suka kewaye gidan, suka yi ta bubbuga ƙofar, suka ce wa tsohon, “Ka fito mana da mutumin da ya zo gidanka don mu yi luɗu!”


Su biyu kuwa suka zauna suka ci suka sha tare. Har yanzu mahaifin mace ya sāke ce masa, “Ina roƙonka ka ƙara kwana, ka saki jikinka ka more.”


Sa'ad da mutumin, da ƙwarƙwararsa, da baransa sun tashi za su tafi, sai mahaifin macen kuma ya ce masa, “Ga shi, rana ta kusan faɗuwa, yamma kuwa ta yi, ina roƙonka, ka sāke kwana ka ji wa ranka dādi, sa'an nan ka yi sammako gobe ka kama hanyarka zuwa gida.”


Rut kuwa ta gangara zuwa masussukar, ta yi yadda surukarta ta faɗa mata.


Da tsakar dare, sai mutumin ya farka a firgice, ya juya, sai ga mace kwance a wajen ƙafafunsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan