Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 3:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Bo'aza wanda kika yi aiki da barorinsa danginmu ne. Ga shi, zai tafi sussukar sha'ir a masussuka da maraice.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Bowaz wanda kike aiki da bayinsa ’yan mata ba danginmu ne na kusa ba? Da daren yau zai sussuka sha’ir nasa a masussuka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 3:2
8 Iomraidhean Croise  

Sa'ad da suka kai farfajiyar masussukar Atad, wanda yake wajen Urdun, a nan ne fa suka yi makoki, da babban makoki da baƙin ciki mai zafi. Aka kuwa yi kwana bakwai ana makokin mahaifinsa.


Na'omi tana da wani dangin mijinta, Elimelek, sunansa Bo'aza, shi kuwa attajiri ne.


Sa'an nan sai Bo'aza ya ce wa Rut, “Kin ji, 'yata, kada ki bar wannan gona ki tafi wata gona domin kala, amma ki riƙa bin 'yan matan gidana.


Wata rana, Na'omi ta ce wa Rut, “'Yata, ya kamata in nemar miki miji don ki sami gida inda za ki huta, ki ji daɗi.


Sai ki yi wanka, ki shafa man ƙanshi, ki yafa tufafinki na ado, ki tafi masussukar, amma kada ki bari ya san zuwanki, sai bayan da ya riga ya ci ya sha.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan