Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 3:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Ki dakata nan sai gobe, da safe za mu gani, idan shi zai cika wajibin dangi na kusa a gare ki. Idan ya cika, to, da kyau, amma idan bai cika ba, na rantse da Allah mai rai, zan cika wajibin dangi na kusa a gare ki. Ki kwanta sai da safe.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Ki kwana a nan, da safe kuwa in yana so yă fansa, to, da kyau, sai yă fansa. Amma in ba ya niyya, tabbatacce, na rantse da Ubangiji mai rai zan yi. Ki kwanta a nan sai da safe.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 3:13
11 Iomraidhean Croise  

Zai zama kuwa, idan za su himmantu su koyi al'amuran jama'ata, su yi rantsuwa da sunana, su ce, ‘Da zatin Ubangiji,’ kamar yadda suka koya wa jama'ata yin rantsuwa da Ba'al, sa'an nan za a gina su a tsakiyar jama'ata.


Idan kun yi rantsuwa kuka ce, ‘Har da ran Ubangiji kuwa,’ Da gaskiya, da aminci, da adalci, Sa'an nan sauran al'umma za su so in sa musu albarka, Za su kuma yabe ni.”


Labudda, Allah shi ne mashaidina a kan cewa, musamman don sawwaƙe muku ne, na fāsa zuwa Koranti.


Hakika mutane sukan rantse da abin da ya fi su, rantsuwa kuma ita ce abar da take tabbatarwa a duk lokacin gardama.


Gidiyon ya ce musu, “Su 'yan'uwana ne, mahaifiyarmu ɗaya. Da ba ku kashe su ba, da ba zan kashe ku ba.”


Na'omi ta ce wa Rut, “Ubangiji wanda bai daina nuna alheri ga masu rai da marigayan ba, ya sa masa albarka.” Ta ƙara da cewa, “Ai, mutumin, shi danginmu ne na kusa.”


Gaskiya ce, ni dangi na kusa ne, amma akwai wanda yake dangi na kusa fiye da ni.


Sa'an nan Bo'aza ya ce, “A ranar da ka sayi gonar daga hannun Na'omi, sai kuma ka ɗauki Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayin, domin ka ta da zuriyar da za ta gaji marigayin.”


Sai dangin nan mafi kusa ya ce, “Ba zan iya ɗaukar Rut ba, domin kada in ɓata nawa gādo. Na bar maka ka ɗauke ta gama ni ba zan iya ba.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan