Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 3:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Gaskiya ce, ni dangi na kusa ne, amma akwai wanda yake dangi na kusa fiye da ni.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Ko da yake gaskiya ne ni dangi ne na kusa, amma akwai dangi mai fansa mafi kusa fiye da ni.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 3:12
7 Iomraidhean Croise  

Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.”


A cikin wannan al'amari kuwa kada kowa ya keta haddi, har ya cuci ɗan'uwansa, domin Ubangiji mai sakamako ne a kan dukkan waɗannan abubuwa, kamar yadda muka gargaɗe ku, muka tabbatar muku tun da wuri.


Na'omi ta ce wa Rut, “Ubangiji wanda bai daina nuna alheri ga masu rai da marigayan ba, ya sa masa albarka.” Ta ƙara da cewa, “Ai, mutumin, shi danginmu ne na kusa.”


Yanzu dai, 'yata, kada ki damu, zan yi miki dukan abin da kika roƙa, gama dukan mutanen garin sun sani ke macen kirki ce.


Ki dakata nan sai gobe, da safe za mu gani, idan shi zai cika wajibin dangi na kusa a gare ki. Idan ya cika, to, da kyau, amma idan bai cika ba, na rantse da Allah mai rai, zan cika wajibin dangi na kusa a gare ki. Ki kwanta sai da safe.”


Bo'aza fa ya tafi, ya zauna a dandalin ƙofar gari. Sai ga wani daga cikin waɗanda hakkinsu ne su ɗauki Rut, shi ne kuwa wanda Bo'aza ya ambata, ya iso. Bo'aza kuwa ya ce masa, “Ratso nan, wāne, ka zauna.” Sai ya ratsa, ya zauna.


Don haka na ga ya kamata in sanar da kai cewa, ka saye ta a gaban waɗanda suke zaune a nan, da a gaban dattawan jama'a. Idan za ka fanshi gonar sai ka fanshe ta, idan kuwa ba za ka fansa ba, ka faɗa mini don in sani, gama daga kai sai ni muke da izinin fansar gonar.” Sai mutumin ya ce, “Zan fanshe ta.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan