Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 3:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Sa'an nan ya ce, “Ubangiji ya sa miki albarka 'yata, yanzu kin nuna alheri mafi girma fiye da na dā da yake ba ki nemi saurayi, matalauci ko attajiri ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Sai ya amsa ya ce, “Ubangiji yă albarkace ki ’yata. Wannan alheri ya fi wannan da kika nuna da farko. Ba ki gudu kin bi saurayi, mai arziki ko matalauci ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 3:10
8 Iomraidhean Croise  

Ya ce masa, “Shigo, ya mai albarka na Ubangiji, don me kake tsaye a waje? Gama na shirya gida da wuri domin raƙuma.”


Amma a hanya, sai Na'omi ta ce wa surukanta, “Bari ko waccenku ta koma gidan iyayenta. Ubangiji ya yi muku alheri kamar yadda kuka yi mini alheri, ni da marigayan.


Amma Bo'aza ya ce mata, “An faɗa mini dukan abin da kika yi wa surukarki tun lokacin da mijinki ya rasu, da yadda kika bar iyayenki da ƙasarku, kika zo wurin mutanen da ba ki taɓa saninsu ba a dā.


Na'omi ta ce wa Rut, “Ubangiji wanda bai daina nuna alheri ga masu rai da marigayan ba, ya sa masa albarka.” Ta ƙara da cewa, “Ai, mutumin, shi danginmu ne na kusa.”


Sai ga Bo'aza ya zo daga Baitalami, ya ce wa masu girbi, “Salamu alaikun.” Suka amsa, “Alaika salamu.”


Ya ce, “Wace ce?” Sai ta amsa, “Ni ce Rut, baranyarka, sai ka rufe ni da mayafinka, gama kai dangi ne na kusa.”


Sai Sama'ila ya tafi wurin Saul, Saul kuwa ya gaishe shi, ya ce, “Ubangiji ya sa maka albarka, Sama'ila, na yi biyayya ga umarninsa.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan