Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 2:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Ita ce ta ce mana, ‘In kun yarda, ku bar ni in bi bayan masu girbin, ina kala.’ Haka ta yi ta kala tun da sassafe har yanzu ba hutu, sai dai 'yar shaƙatawar da ta yi kaɗan.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ta ce, ‘Ina roƙo a bar ni in bi bayan masu girbin in yi kala.’ Haka ta shiga cikin gonar ta kuwa yi aiki tun da safe har zuwa yanzu, sai ɗan hutun da ta yi kaɗan.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 2:7
14 Iomraidhean Croise  

Rago yakan ƙosa ya sami wani abu ainun, amma sam, ba zai samu ba. Mai mai da hankali ga aikinsa zai sami kowane abu da yake bukata.


Tsoron Ubangiji koyarwa ce domin samun hikima. Sai ka zama mai tawali'u kafin ka sami girmamawa.


Matalauci yakan yi roƙo da taushi, maganar matalauci rarrashi ne, amma attajiri yakan yi magana garas.


Ka nuna mini mutumin da yake aiki mai kyau, ni kuwa in nuna maka mutumin da ya fi duka, wanda ya cancanci ya zauna tare da sarakuna.


Duk abin da kake iya yi, ka yi shi da iyakar iyawarka, domin ba aiki, ko tunani, ko ilimi, ko hikima a lahira, gama can za ka.


“Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu, domin Mulkin Sama nasu ne.


Kada ku sassauta a wajen himma, ku himmantu a ruhu, kuna bauta wa Ubangiji.


Kada mu yi sanyi da yin aiki nagari, don za mu yi girbi a kan kari, in ba mu karai ba.


Ku bi juna saboda ganin girman Almasihu.


Sai Rut, mutuniyar Mowab, ta ce wa Na'omi, “Bari in tafi, in yi kalan hatsi a gonar wanda ya yarda in yi.” Na'omi ta ce mata, “Ki tafi, 'yata.”


Rut kuma, mutuniyar Mowab, ta ce, “Banda wannan ma, ya ce mini, ‘Ki riƙa bin barorina, har lokacin da suka gama mini girbin.’ ”


Baran ya ce, “Ita 'yar Mowab ce wadda ta zo tare da Na'omi daga ƙasar Mowab.


Sa'an nan sai Bo'aza ya ce wa Rut, “Kin ji, 'yata, kada ki bar wannan gona ki tafi wata gona domin kala, amma ki riƙa bin 'yan matan gidana.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan